"Ina da N12m a Cikinsa: Matashi Ya Koka Bayan An Goge Masa Asusu, Ya Nuna Shaida

"Ina da N12m a Cikinsa: Matashi Ya Koka Bayan An Goge Masa Asusu, Ya Nuna Shaida

  • Wani mutumi ya ce an goge asusunsa na Binance mai sama da $15,000 a ciki, ba tare da wani dalili ba
  • Matashin mai suna @biggerisgreat, ya shiga shafin Twitter inda ya bayyana kokensa tare da kiran kamfanin
  • Ya ce ko bayan an dawo da asusun, sai ya gano babu komai a cikinsa, tare da duk kuɗin da ke cikin sa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani matashi ya koka a shafukan sada zumunta, yana mai cewa an goge masa asusun Binance ɗinsa ba tare da wani dalili ba.

Mutumin, @biggerisgreat, ya yi iƙirarin cewa asusun yana da sama da $15,000 a ciki. Wannan dai ya haura sama da Naira miliyan 12 a farashin canji na yau.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ɗan kwallon Najeriya Musulmi ya yanke jiki ya faɗi a filin atisaye, Allah ya masa rasuwa

Matashi ya koka kan batan kudinsa
Matashin ya ce akwai N12m a asusunsa Hoto: Twitter/@biggerisgreat and Getty Images/Bloomberg.
Asali: UGC

Cikin takaici mutumin ya tuntuɓi Binance, kuma aka dawo da asusun, amma ya gano cewa babu kuɗi a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Naira miliyan 12 da ke cikin asusun ta ɓace. Ga kawo lamarin a shafin Twitter, inda ya rubuta:

"Wane laifi na yi muku da kuka goge asusuna da sama da dalar Amurka dubu 15 a ciki sannan kuma bayan wakilinku ya taimaka min wajen dawo da asusun, ban iya samun kuɗina ba ko tarihin asusuna ba."

Binance ya yi martani

A cikin wani martanin gaggawa, Binance ya tabbatar da yin magana da mutumin bayan ya gabatar da ƙorafi.

Kamfanin ya ce:

"Bayan bin diddigin bayanan da suka shafi ID da ka gabatar, da alama tawagar mu ta amince ta sake dawo da asusun ka a ƙarshen tattaunawar da muka yi a baya, kuma muna jiran tabbatarwar ka."

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

@worldpicin ya rubuta:

"Da farko ka gaya mana abin da ka yi, domin yawancin masu siyan nan suna tunanin kowa sakarai ne, a haka ne wani mutum ya ƙi biya na kuma ya riga ya sanya a cinikin ya biya, duk ƙoƙarin da na yi don samun wannan gayen amma ya ci tura, sai ya ɗauka ni sabon shiga ne. Sai na shigar da ƙorafi, nan da nan ya yi sauri ya soke."

@Chubbygoddesss ya rubuta:

"Da alama an yi kutse a cikin asusunka saboda yadda masu kula da kwastomomi su ke ba ka amsa babu ƙwarewa a ciki."

Dan Najeriya Ya Caccaki Bankinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan Najeriya ya koka bayan bankinsa ya lafke shi da kuɗaɗen jabu.

Ɗan Najeriyan ya bayyana cewa an ba shi tsabar kuɗi Yuro 5,000 na jabu, kuma ya gano ne kawai lokacin da abokinsa ya je canja kuɗin zuwa fam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng