Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shirya gudanar da taron kwamitin zartaswa na kasa. Za a fafata tsakanin Atiku da Wike kan shugabancin jam'iyyar.
Gidauniyar Murtala Muhammad Foundation (MMF) ta fitar da rahito kan yadda 'yan matan Chibok da aka sako suka dawo da yara 34, wasu daga cikin iyayensu sun rasu.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) ta cafkw wata 'yar siyasa ta hannun daman Nasir Ahmad El-Rufai a jihar Kaduna.
Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu, ya yi karin haske kan halin da jarumin masana'antar Kannywood, Adam A. Zango ya samu kansa a ciki.
Hukumar EFCC ta sanar da cewa binciken da take yi a ma'aikatar jinkai da yaki da fatara ya sanya ta gano makudan kudaden da aka wawushe daga ma'aikatar.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a jihar Zamfara. Sojojin sun kashe mutum 12 tare da kwato makamai.
Kasar Isra'ila ta yi martani kan harin da Iran ta kai mata a cikin kasarta. Wani jami'in gwamnati ya ce nan da jimaw ba Iran za ta ji daba gare su.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ya cika dukkanin alkawuran da ya daukarwa al'ummar jihar Katsina a lokacin yakin neman zabe.
Gwamnatin jihar Borno ta tuna da ragowar 'yan matan Chibok da ke tsare a hannun Boko Haram. Gwamnatin ta sha alwashin ceto su domin sada su da iyalansu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari