Bayan Matawalle Wata Kungiya Ta Caccaki Dattawan Arewa Kan Sukar Shugaba Tinubu

Bayan Matawalle Wata Kungiya Ta Caccaki Dattawan Arewa Kan Sukar Shugaba Tinubu

  • An sake taso ƙungiyar Dattawan Arewa a gaba kan sukar da suka yi wa shugaban ƙasa watau Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Wata ƙungiya ta matasan yankin Arewacin Najeriya ta yi tir da barazanar da Dattawan na Arewa suka yi wa shugaban kasa
  • Ƙungiyar ta buƙace su da su riƙa bada shawarwari masu kyau kan yadda za a ciyar da ƙasar nan gaba maimakon sukar gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar 'North Eastern Youths Advocacy for Peace and Development' ta raba gari da ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) kan sukar Shugaba Bola Tinubu.

Ƙungiyar NEF dai ta yi barazanar cewa yankin Arewacin Najeriya ba zai zaɓi Shugaba Tinubu ba a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

APC ta yi fatali da batun dakatar da Ganduje, ta dauki mataki kan masu hannu a ciki

An caccaki Dattawan Arewa
An bukaci Dattawan Arewa su bar Tinubu ya yi aikinsa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Tinubu: An caccaki Dattawan Arewa

Ƙungiyar a cikin wata sanarwa da jagoranta, Salahudeen Shuaibu ya fitar, ta caccaki NEF bisa kalaman da ta yi a kan Shugaba Tinubu, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana kalaman na NEF a matsayin wani yunƙuri na ƙoƙarin kawar da hankalin shugaban ƙasan daga aiwatar da abin da aka zaɓe shi ya yi.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa Shugaba Tinubu ya yi aiki tuƙuru tun bayan hawansa mulki domin farfaɗo da tattalin arziƙi, samar da tsaro, inganta ilmi da noma da dawo da darajar Najeriya a idon duniya.

Salahudeen ya bayyana cewa kamata ya yi a yaba da ƙoƙarin shugaban ƙasan maimakon yin Allah wadai da su, shafin Koko tv ya tabbatar.

Ya yi gargaɗin cewa matasan yankin Arewa ta Gabas ba za su sake yarda a ci mutuncin shugaban ƙasan ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 12 a wani sabon hari

Wace shawara aka ba Dattawan Arewa?

Ƙungiyar ta kuma buƙaci dattawan Arewa da su bayar da shawarwari masu kyau da za su taimaka wajen ciyar da ƙasar nan gaba, maimakon yin kalamai marasa daɗi a kan ƙasar nan.

Sun yi gargaɗin cewa babu wani amfani da za a samu idan aka aibanta ƙimar shugaban ƙasa da ƙasar baki ɗaya.

Ƙungiyar ta kuma goyi bayan ƙaramin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle, kan sukar da ya yi wa dattawan Arewa.

Matawalle ya ƙalubalanci ƴan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ƙalubalanci dukkan wadanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa mukami a Arewa.

Matawalle ya ce ya kamata dukkansu su fito su kare shugaban yayin da ya ke fuskantar kushewa da suka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel