Binciken Ma'aikatar Ministan Tinubu Ya Sanya EFCC Ta Kwato N32bn

Binciken Ma'aikatar Ministan Tinubu Ya Sanya EFCC Ta Kwato N32bn

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta yi ƙarin haske kan binciken da take yi a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara
  • EFCC ta yi nuni da cewa ya zuwa yanzu binciken ya sanya ta ƙwato N32bn, $445,000 da aka wawushe daga ma'aikatar
  • Kakakin hukumar mai yaƙi da cin hancin, Dele Oyewale, ya bayyana hakan a ciikim wata sanarwa da ya fitar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta ce ta ƙwato N32.7bn da $445,000 da ake zargin wawushe a ma'aikatar jinƙai da yaƙi da fatara.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a shafin X da kakakinta, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alkawarin rage farashin man fetur zuwa N100? Gaskiya ta bayyana

Hukumar EFCC ta kwato N32bn
Binciken EFCC ya sanya ta kwato N32bn a ma'aikatar jinkai Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

EFCC ta fito ta bayyana hakan ne bayan abin da ta kira yadda ake ta yawan maganganu kan binciken da take yi a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyewale ya yi bayanin cewa a farkon binciken da hukumar ta fara, ta gayyato tsofaffi da dakatattun jami'an ma'aikatar domin jin daga bakinsu.

Wane bincike EFCC take gudanarwa?

A cewar kakakin na EFCC, hukumar ta kuma fara binciken wasu ayyukan zamba da suka haɗa bashin da aka ciyo daga bankin duniya, kuɗaɗen Covid-19 da kuɗaɗen da aka karɓo na Abacha waɗanda aka ba ma'aikatar domin rage raɗaɗin talauci.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A farkon fara bincike, an gayyato tsofaffi da dakatattun jami'an ma'aikatar jinƙai, kuma binciken da ake yi kan zargin zamba ya sanya ya zuwa yanzu an ƙwato N32.7bn da $445,000."

Kara karanta wannan

Kungiya ta ja kunnen Gwamna Abba kan binciken Ganduje, an ba shi shawarar abin da ya kamata ya yi

"Binciken kuma ya bankaɗo jami'an ma'aikatar masu yawa waɗanda ake zargin da hannunsu wajen yin sama da faɗi da kuɗaɗen."
"Yana da kyau a bayyana cewa binciken hukumar ba ana yinsa ba ne kan wasu mutane. EFCC na binciken ayyukan zamba ne masu yawa da aka aikata. Bankuna da ke hannu a ciki na fuskantar bincike."

Tsohon minista ya kai ƙarar EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan makamashi da ƙarafuna, Olu Ogunleye, ya shigar da ƙara kan hukumar EFCC a gaban kotu.

Tsohon ministan ya ɗauki wannan matakin ne.bayan hukumar ta wallafa sunansa a cikin mutanen da ake nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel