Atiku vs Wike: An Yi Hasashen Abin da Zai Faru a Wajen Taron NEC Na PDP

Atiku vs Wike: An Yi Hasashen Abin da Zai Faru a Wajen Taron NEC Na PDP

  • Demola Olarewaju na jam'iyyar PDP ya yi hasashen cewa ba za a yi cacar baki ba a taron NEC da za a yi na jam'iyyar ba
  • Olarewaju ya ce babban abin da ƴan Najeriya ke buƙata daga taron NEC ya wuce rigimar Atiku Abubakar da Nyesom Wike
  • Babban taron na majalisar NEC na jam'iyyar PDP za a gudanar da shi ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta shirya gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairun 2024.

Taron dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rigima tsakanin sansanin Atiku Abubakar da na Nyesom Wike kan shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

PDP za ta gudanar da taron NEC
Atiku da Wike za su hadu wajen taron NEC Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Ezenwo Wike - GSSRS, CON
Asali: Facebook

Demola Olarewaju, mataimaki na musamman kan kafafen sadarwa na zamani ga Atiku, a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa PDP ba ta da tsara saboda ta gudanar da taron NEC sau 98 tun daga shekarar 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP: Me hadimin Atiku ya ce kan taron NEC?

Olarewaju ya kuma bayyana cewa lokacin yin cacar baki a wajen taron NEC na PDP ya riga da ya wuce.

Ya dai bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

"Ga wadanda ke jiran a yi cacar baki daga wannan taron, kwanakin hakan sun shuɗe."
"A yanzu tarurrukan NEC ana yin su ne bayan an yi na ƙungiyar ƴan majalisu, ƙungiyar gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki har zuwa kan taron kwamitin amintattu na ƙasa."

Kara karanta wannan

Ana fargabar rasa rai yayin da miyagu suka farmaki ɗan takarar gwamna

"Babban abin da ƴan Najeriya ke tsammani a wannan taron NEC na PDP karo na 98 ya wuce Atiku ko Wike ko kuma wani"
"Abin da ake jira shi ne mu ji amsar da PDP za ta bayar ga wata tambaya mai sauƙi: “Shin kun shirya ku zama ƴan adawa, ko kuwa?"

- Demola Olarewaju

Hanyar warware rikicin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan majalisun PDP a majalisar wakilai ta yi magana kan hanyoyin warware rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.

Ƙungiyar ta yi kira ga fusatattun ƴaƴan jam'iyyar da su janye dukkanin ƙararrakin da suka shigar domin a yi sulhu a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel