An Samu Tashin Mummunar Gobara a Babbar Kasuwar Jihar Adamawa

An Samu Tashin Mummunar Gobara a Babbar Kasuwar Jihar Adamawa

  • Asara ta gitta kan ƴan kasuwa a garin Yola bayan an samu tashin wata mummunar gobara cikin kasuwa
  • Gobarar wacce ta tashi dai ta yi sanadiyyar lalata shaguna masu yawa waɗanda ba a tantance yawansu ba
  • Mataimakiyar gwamnan jihar ta ziyarci kasuwar domin nuna alhihini da yin jaje ga waɗanda lamarin ya ritsa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - An samu tashin mummunar gobara a kasuwar garin Yola da sanyin safiyar ranar Litinin.

Gobarar wacce ta tashi a kasuwar da ke ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ta lalata shaguna masu yawa, cewar rahoton jaridar Leadership.

Gobara ta tashi a Adamawa
Gobara ta lalata shaguna masu yawa a kasuwar Yola Hoto: @fedfireng
Asali: Facebook

Mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta ziyarci kasuwar da gobarar ta auku da safiyar ranar Litinin, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farauta ta bayyana cewa har yanzu ba a tantance girman ɓarnar da gobarar ta yi ba, inda ta yi alƙawarin ba ƴan kasuwar da abin ya shafa tallafi.

Wane mataki gwamnati za ta ɗauka?

Farauta ta ce duk da ba a tantance adadin ƴan kasuwar da lamarin ya shafa ba, gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin rage musu raɗaɗi.

A kalamanta:

"Mun zo nan ne domin yi wa ƴan uwanmu maza da mata jaje waɗanda wannan gobarar ta shafa."
“Gwamnati za ta duba musabbabin abin da ya haifar da gobarar yayin da har yanzu ba a tantance adadin shagunan da suka ƙone ba."

Ta buƙaci ƴan kasuwar da su ɗauki ƙaddara kan gobarar tun da ba a rasa ran ko mutum ɗaya ba.

Shugaban ƴan kasuwar, Umar Abubakar, ya buƙaci gwamnati ta kawo musu ɗauki, inda ya bayyana cewa gobarar ta jawo ƴan kasuwa da dama sun rasa wuraren neman abincinsu.

Kara karanta wannan

Iftila'i: Mummunar gobara ta shafe kasuwar Boda dake Gaya

Gobara ta laƙume shaguna

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tafka asara mai tarin yawa bayan mummunar gobara ta tashi a kasuwar Balogun da ke Legas.

Gobarar wacce ta tashi a ɓangaren sayar da kayan kwalliya na kasuwar ta jawo asarar kayayyaki na biliyoyin Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel