Sukar Gwamna Uba Sani Ya Sanya Ta Hannun Daman El-Rufai Shiga Komar DSS

Sukar Gwamna Uba Sani Ya Sanya Ta Hannun Daman El-Rufai Shiga Komar DSS

  • Wata ƴar siyasa da ke tare da jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta faɗa hannun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS)
  • Jami'an hukumar sun yi caraf da Aisha Galadima wacce ta hannun daman Nasir Ahmad El-Rufai ce bayan ta caccaki Gwamna Uba Sani
  • Sai dai, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan kamun da aka yi wa wannan ƴar jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jami'an hukumar DSS sun cafke wata ƴar siyasa ta jam'iyyar APC, Aisha Galadima, a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an cafke ƴar siyasar wacce ta hannun daman tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai ce a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

Kungiya ta ja kunnen Gwamna Abba kan binciken Ganduje, an ba shi shawarar abin da ya kamata ya yi

DSS ta cafke ta hannun daman El-Rufai
Aisha Galadima: An cafke mutumiyar El-Rufai bisa zargin sukar Uba Sani a Kaduna Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa kamun da aka yi mata na da nasaba da wani rubutu da ta yi a soshiyal midiya kan gwamnan jihar Malam Uba Sani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyoyi, Aisha Galadima ta caccaki Gwamna Uba Sani bisa kalaman da ya yi kan Nasir El-Rufai, a shafinta na Facebook.

Wani maƙwabcinta ya bayyana cewa an cafke ta ne a gidanta da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi, yayin da wata ƙawarta ta ce an kashe wayoyinta bayan kamun da aka yi mata.

Gwamnati na da masaniya kan kama Aisha?

Sai dai, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kaduna, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya kan kamun da aka yi mata.

Shehu ya yi nuni da cewa a tuntuɓi hukumar tsaron farin kaya ta DSS domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya caccaki dattawan Arewa kan kalaman da suka yi game da Bola Tinubu

A kalamansa:

"Ba ni da masaniya cewa an kama wata mata saboda ta caccaki mai girma gwamna. Koma dai menene ku tuntuɓi hukumar DSS ba gwamnatin jihar Kaduna ba."

Yaron El-Rufai ya soki Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa yaron tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir Nasir El-Rufai, ya caccaki Gwamna Uba Sani kan batun bashin da ya ce ya gada a wajen El-Rufai.

Bashir ya yi nuni da gwamnan na ƙoƙarin fakewa ne da gaza taɓuka komai da ya yi tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel