JD Vance Ya Fito da Gaskiya, An Ji Matakin Iran da Ya Fi Cutar da Amurka a Lokacin Yaki
- Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya tuna matakin da Iran ta dauka wanda ya girgiza kasar da sauran kasashen duniya
- Vance ya bayyana matakin rufe mashigar ruwa ta Hormuz da Iran ta yi lokacin yaki a matsayin ta'addancin tattalin arziki
- Ya kuma jaddada cewa bayan tattaunawar da suka yi a Islamabad, yanzu wuka da nama na hannun Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
America - Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya zargi Iran da aikata abin da ya kira “ta’addancin tattalin arziki” bayan katse zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Iran dai ta hana jiragen dakon mai na Amurka da Isra'ila da duk wasu kasashen da ke goyon bayansu, wucewa ta mashigar ruwan a lokacin yakin da suka yi na akalla kwanaki 40.

Source: Getty Images
Vance ya koka kan rufe mashigar Hormuz

Kara karanta wannan
Akwai gagarumar matsala, Iran ta sanar da asarar da ta tafka a yakin Amurka da Isra'ila
Da yake magana da tashar Fox News, Vance ya ce matakin da Iran ta dauka na barazana ga jiragen ruwa da ke bi ta wannan muhimmiyar mashiga, ya shafi Amurka da duniya baki daya.
“Abin da suka yi shi ne ta’addancin tattalin arziki ga duniya baki daya. Suna barazana ga duk wani jirgi da ke wucewa ta Strait of Hormuz,” in ji shi.
Ya kara da cewa Amurka ma za ta iya daukar irin wannan mataki, yana mai gargadin cewa idan Iran ta ci gaba da hakan, to ba za a bar jiragen ruwanta su fita ba.
Amurka da Iran sun fara fahimtar juna
Vance ya kuma bayyana cewa an samu “kyakkyawar tattaunawa” tsakanin Amurka da Iran a Pakistan a karshen mako, duk da cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba.
Lokacin da aka tambaye shi ko za a ci gaba da tattaunawa, ya ce wuka da nama na hannun Iran, yana mai cewa ita ce ke da alhakin daukar mataki na gaba.
“Akwai yiwuwar a samu babbar yarjejeniya, amma komai na hannun Iran. Su ne za su dauki mataki na gaba,” in ji shi
Abin da Amurka ta fi damuwa da shi
Ya jaddada cewa Amurka na bukatar a fitar da sindarin uranium daga Iran, tare da samun tabbacin cewa kasar ba za ta kera makamin nukiliya ba.
Mataimakin shugaban Amurka ya kara da cewa:
“Muna bukatar a cire uranium din daga Iran, kuma muna bukatar cikakken tabbaci cewa ba za su kera makamin nukiliya ba."

Source: UGC
A cewarsa, Iran ta nuna sassauci a tattaunawar, amma bai kai matsayin da ake bukata ba, yana mai cewa idan Iran ta amince da sharudan Amurka, hakan zai iya haifar da yarjejeniya mai anfani ga bangarorin biyu
Sai dai idan ba ta amince ba, ya ce hakan zabi ne da Iran za ta dauka, tare da sakamakon da zai biyo baya, kamar yadda tashar NBC News ta ruwaito.
Iran ta nemi diyya daga kasashe 5
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta sake jaddada bukatarta ta neman diyyar barnar da aka mata a yakin da ya gudana tsakaninta da Amurka da Isra'ila.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saed Iravani ne ya bayyana hakan, yana mai cewa kasar na neman diyya daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Iravani ya ce Iran na neman diyya daga kasashen Bahrain, Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jordan saboda zarginsu da taimaka wa Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

