Isra'ila Ta Fadi Lokacin da Za Ta Rama Harin da Iran Ta Kai Mata

Isra'ila Ta Fadi Lokacin da Za Ta Rama Harin da Iran Ta Kai Mata

  • Isra'ila ta sha alwashin cewa Iran za ta ji ta bakin dakarunta bayan jiragen Iran marasa matuƙa da makamai masu linzami sun kai hari a ƙasar a daren ranar Asabar
  • Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ya bayyana shirin, inda ya ƙara da cewa har yanzu ƙasar ba ta tantance matakin da za ta ɗauka a matsayin ramuwar gayya ba
  • A wani hari da ta kai, Iran ta tabbatar da harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami sama da 300 a yankin Isra'ila cikin dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Isra'ila ta ce za ta mayar da martani kan harin da jirage marasa matuƙa na Iran da makamai masu linzami suka kai mata da zarar ta kammala nazari kan yanayin harin.

Kara karanta wannan

"Ba mu ciki": Amurka ta bayyana matsayarta kan rikicin Iran da Isra'ila, ta yabawa sojoji

A cewar CNN, wani jami'in Isra'ila ya ce har yanzu mahukunta a Tel Aviv ba su tantance martanin da ya dace su yi ba.

Iran ta kai hari kan Isra'ila
Isra'ila za ta dauki fansa kan Iran Hoto: Contributor, Sean Gallup
Asali: Getty Images

Wane mataki Isra'ila za ta ɗauka?

Suna shawara kan yin ramuwar gayya mai zafi ko kuma bin lamuran cikin ruwan sanyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra'ila ta yi iƙirarin cewa an harbo jirage marasa matuƙa 300 da makamai masu linzami daga Iran, Iraq da Yemen, inda ta ƙara da cewa sojojinta sun kakkaɓo mafi yawancinsu.

Iran ta bayyana cewa, an kai harin ne a matsayin ramuwar gayya kan farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a ofishin jakadancinta da ke Syria a a ranar 1 ga watan Afrilun 2024.

A cewar mahukunta a Iran, harin da a aka kai Isra'ila ya sanya an kawo ƙarshen batun.

Matsayar Amurka kan rikicin Iran da Isra'ila

Kara karanta wannan

Iran ta kai hari kan Isra'ila, ana fargabar barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya bayyana matsayarsa kan rikicin Iran da Isra'ila.

Biden ya tabbatarwa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu cewa ba zai shiga faɗan Iran da ƙasar ba.

Shugaban ƙasan na Amurka ya yi wannan furuci ne biyo bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai a kan Isra'ila cikin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel