Sanata Ya Fadi Lokacin da Zai Ɗauki Tinubu Ya Murkushe Ƴan Bindiga idan Yana So

Sanata Ya Fadi Lokacin da Zai Ɗauki Tinubu Ya Murkushe Ƴan Bindiga idan Yana So

  • Sanata Ali Muhammad Ndume ya bayyana yadda gwamnatin Najeriya za ta kawo karshen ta'addanci idan ta shirya da gaske
  • Ndume ya ce gwamnatin na da ikon kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin watanni shida idan ta nuna ƙwazo, jajircewa da daukar matakai
  • Sanatan ya nuna damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a Arewa maso Gabas da sauran yankuna, yana mai cewa matsalar ba ta kuka ba ce

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Muhammad Ndume, ya yi magana game da kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ndume ya bayyana cewa Najeriya na da damar kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin watanni shida kacal idan gwamnatin tarayya ta nuna ƙwazo da ɗaukar matakai masu tasiri.

Ndume ya nuna damuwa game da karuwar ta'addanci a Najeriya
Sanata Ali Ndume yayin zaman majalisa a Abuja. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Source: Facebook

Ali Ndume ya kawo mafita kan rashin tsaro

Kara karanta wannan

An tashi baram baram: Amurka da Iran sun kasa fahimtar juna, ana iya komawa yaki

Ndume ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi da yan jaridu wanda jaridar The Sun ta bibiya.

Sanatan ya nuna damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.

A cewarsa, kawo ƙarshen rashin tsaro ba wai magana ce kawai ba, sai an nuna jajircewa wajen horas da sojoji, samar musu da kayan aiki, makamai da kuma ƙarfafa musu gwiwa.

Ya ce:

“Ba batun korafi ba ne. Idan shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya suna da niyyar gaskiya, za a iya kawo ƙarshen wannan matsala cikin watanni shida.”

Zargin da Ndume ke yi kan matsalolin tsaro

Sanatan na Borno ya yi tir da yadda ake ci gaba da rasa rayukan jami’an tsaro, ciki har da manyan jami’ai, yana mai cewa hakan na nuna akwai matsaloli a tsarin aiki da ya kamata a gyara cikin gaggawa.

Ya kuma dora alhakin matsalar tsaro kan rashin bin tsare-tsaren da aka amince da su a baya, yana mai cewa dole ne gwamnati ta tabbatar da aiwatar da manufofi yadda ya kamata domin samun sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Kashe kashe a Najeriya ya damu Atiku sosai, ya yaba wa gwamnatin Amurka

Sanata Ndume ya zargi tsare-tsaren gwamnatocin baya kan matsalar tsaro
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Source: Twitter

Shawarar Ndume ga Gwamnatin Najeriya

Ndume ya bukaci a ƙara amfani da bayanan sirri, fasaha, jiragen sama marasa matuki da ƙwararrun dabarun yaki maimakon dogaro da taimakon ƙasashen waje kawai, cewar TheCable.

“Abin da muke buƙata shi ne bayanan sirri. Muna buƙatar tallafin sama da kuma ƙwarewa. Mun riga muna da ƙwararrun jami’ai a ƙasa; abin da suke buƙata kawai shi ne kayan aiki, alburusai da kuma ƙarfafa gwiwa.”

- Ali Ndume

A ƙarshe, ya yaba wa Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen daidaita al’amura a wasu yankunan jihar duk da ƙalubalen ta’addanci.

Ndume ya shawarci Tinubu kan harin Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Ali Ndume ya fadawa Shugaba Bola Tinubu cewa tsaron rayukan 'yan Najeriya ya fi siyasar 2027 muhimmanci.

Ndume ya nemi Tinubu ya ziyarci Borno ko ya tura mataimakinsa domin jajanta wa iyalan mutane 25 da bam ya kashe.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi magana game da wadanda harin bama-bamai ya kashe a Maiduguri inda ya sha alwashin kawo kashen rashin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com