Yadda 'Yan Matan Chibok Suka Dawo da Yara 34 Bayan Boko Haram Sun Sako Su

Yadda 'Yan Matan Chibok Suka Dawo da Yara 34 Bayan Boko Haram Sun Sako Su

  • An cika shekara 10 da sace ƴan matan Chibok, yayin da har yanzu wasu ke tsare a hannun ƴan ta'addan Boko Haram
  • Wasu daga cikin ɗaliban da aka sako sun dawo gida da yara, kamar yadda gidauniyar Murtala Muhammed Foundation ta bayyana
  • Gidauniyar ta koka matuƙa dangane da auren dole da aka yi wa ƴan matan, yayin da suka gabatar da buƙatarsu a gaban gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An fitar da wani sabon rahoto shekara 10 bayan sace ɗalibai 276 daga makarantar sakandaren ƴan mata ta Chibok a jihar Borno.

Rahoton ya nuna cewa ƴan mata 21 daga cikin waɗanda aka sako ya zuwa yanzu sun zo gida tare da yara 34.

Kara karanta wannan

Zamfara: Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 12 a wani sabon hari

'Yan matan Chibok sun dawo da yara
An yi shekara 10 da sace 'yan matan Chibok Hoto: The New York Times, BBC
Asali: Facebook

Gidauniyar Murtala Muhammed (MMF) ta bayyana haka a wani rahoto da ta rabawa manema labarai a ƙarshen mako a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa ƴan matan Chibok auren dole

Jaridar Nigerian Tribune ta ce rahoton an yi shi ne domin tunawa da cika shekaru 10 da sace ƴan matan.

Rahoton ya tabbatar da cin zarafi da auren dole da ƴan matan suka fuskanta a lokacin da suke tsare a hannun ƴan ta'addan.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, rahoton na gidauniyar ya ƙara bayyana cewa iyayen ɗaliban aka sace su 48 ne suka mutu.

Sauran iyayen ɗaliban da ke raye kuma na rayuwa cikin tashin hankali da fargabar rashin sanin halin da ƴaƴansu ke ciki.

Chibok: Wace shawarwar MMF ta bada?

Daraktan MMF, Dakta Aisha Muhammad-Oyebode wacce ta gabatar da rahoton ta bayyana cewa gidauniyar ta lissafa wasu muhimman shawarwari guda 10.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta sha alwashin ceto ragowar 'yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram

Gidauniyar ta ce ya kamata gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙasashen duniya su bada fifiko a kan wadannan shawarwari.

Shawarwarin sun haɗa da, ɗaukar ingantattun matakan tsaro, shirye-shiryen tallafawa ƙauyuka da tsarin ankararwa cikin gaggawa dangane da barazanar tsaro.

Batun ceto ƴan matan Chibok

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta yi magana kan batun ceto ragowar ƴan matan Chibok da ke hannun Boko Haram.

Gwamnatin ta bayyana cewa tana aiki tare da jami'an tsaro domin kuɓutar da ragowar ɗaliban da ke tsare a hannun ƴan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel