Zamfara: Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ya'adda 12 a Wani Sabon Hari

Zamfara: Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Ya'adda 12 a Wani Sabon Hari

  • Dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta Operarion Hadarin Daji sun samu nasarar ragargazar ƴan ta'adda a Zamfara
  • Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan a wasu ƙauyuka uku na jihar inda suka kashe mutum 12
  • Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar ƙwato makamai masu yawa daga hannun masu tada ƙayar bayan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) a yankin Arewa maso Yamma, sun kashe ƴan ta'adda 12 a jihar Zamfara.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai, da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47, jigida guda ɗaya, harsasai biyu masu kaurin 7.62mm da shanu guda 18, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke mutum 6 masu yi wa 'yan ta'adda safarar kayayyaki a Borno

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
Sojoji sun yi galaba kan 'yan ta'adda a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Suleman Omale, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Asabar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omale ya ce nasarar da aka samu ta biyo bayan ci gaba da kai hare-hare kan ƴan ta'adda masu tada ƙayar baya domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

Yadda sojoji suka sheƙe ƴan ta'addan

Ya ce sojojin sun samu nasarar mamaye ƙauyukan Babban Doka, Gobirawar Challi da Kabaro a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Maru a jihar, inda suka yi artabu da ƴan ta’addan a ranar Juma’a.

A kalamansa:

"A yayin wannan samame sojojin mu na yankin Dansadau sun nuna jarumtaka ta musamman, inda suka yi galaba a kan ƴan ta’addan tare da kashe mutum 12, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga."

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 150, sun samu nasarori a Arewacin Najeriya

"Sojojin sun ƙwato manyan makamai da kadarori daga wurin, ciki har da bindiga AK-47 guda ɗaya, jigida guda ɗaya, alburusai biyu na musamman masu kaurin 7.62mm, bindigar gida guda ɗaya."
"Bugu da ƙari, sojojin sun kuma kwato shanu 18, babura 10 na ƴan ta’addan tare da lalata su nan take."

Omale ya ce kwamandan sashe na ɗaya na ɗaya na OPHD, Birgediya Janar Sani Ahmed ya yaba da jajircewa tare da ƙwazon da sojojin suka nuna.

Sojoji sun cafke ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dakarun sojoji sun cafke aƙalla mutum shida masu yi wa ƴan ta'addan Boko Haram safarar kayayyaki a jihar Borno.

Sojojin sun cafke ɓata garin ne tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro a ranar Asabar, 13 ga watan Afirilun 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel