Amurka Ta Toshe Hormuz, Kim Jong Un Ya Harba Makamai Masu Iya Harbo Jirage
- Rahotanni sun nuna cewa Koriya ta Arewa da Kim Jong Un ke jagoranta ta gwada wasu manyan makamai masu linzami zuwa wani teku
- Bayanan da kasar ta fitar sun nuna cewa Kim Jong Un da kan shi ya halarci gwajin makaman tare da wasu manyan jami'an gwamnatinsa
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da fuskantar barazanar tsaro a duniya biyo toshe Hormuz ta Amurka ta ce ta yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT - Koriya ta Arewa ta gudanar da wani sabon gwajin makamai masu linzami da kuma makamai masu kai hari kan jiragen ruwa.
An sanar da cewa kasar ta bayyana hakan a matsayin wani bangare na gwajin jirgin ruwanta mai suna Choe Hyon, kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan
"Ba mu yarda ba," Malaman Musulunci sun tunkari gwamna kan 'tsarin' da ya kawo a Najeriya
Rahoton Reuters ya nuna cewa shugaba Kim Jong Un ya halarci gwajin tare da manyan jami’an tsaro da kwamandojin rundunar ruwa.
Kim Jong Un ya harba makamai
Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami biyu da kuma wasu uku na kai hari kan jiragen ruwa domin duba tsarin kula da makaman wani jirginta.
An bayyana cewa hakan na cikin shirin horar da ma’aikata kan yadda ake harba makamai, da kuma tabbatar da inganci da kariya daga katsalandan da za su iya samu.
Rahoton ya ce makaman sun yi tafiya ta tsawon dakika 7,869 zuwa 7,920, yayin da makaman kai hari kan jiragen ruwa suka yi tafiya na tsawon dakika 1,960 zuwa 1,973 a saman ruwa a gabar yammacin kasar.
NBC ta wallafa cewa biyo bayan harba su, Koriya ta Arewa ta sanar da cewa makaman kai hari kan wuraren da aka nufa ba tare da samun wata tangarda ba.
Harba makaman sun biyo bayan matakin da Donald Trump ya dauka na toshe wata hanya da ke da alaka da mashigar ruwan Hormuz saboda gaza cimma yarjejeniya da Iran.
Bayanin da aka yi wa Kim Jong Un
Kasar ta sanar da cewa an gabatar wa Kim Jong Un bayanai kan shirin tsarin makamai a wasu jiragen yaki guda biyu da ake kerawa, wanda ke nuna shirye-shiryen kera jirgi na uku da na hudu samfurin Choe Hyon.
Kim ya ce karfafa karfin dakile yaki da nukiliya na kasar na daga cikin manyan manufofinsa, tare da kira da a inganta shirin kai hari a lokutan gaggawa da kuma shirin daukar mataki cikin sauri.

Source: Getty Images
Koriya ta Arewa ta fara gwajin makamai a kan jirgin ruwan yaki mai nauyin tan 5,000 na samfurin Choe Hyon a watan Afrilu 2025, sannan a watan Yuni Kim ya sanar da shirin kera wasu karin jirage biyu a shekarar 2026.
Za a hana sayarwa Isra'ila makami
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Isra'ila za ta iya fuskantar barazanar tsaro ko karancin kayan yaki yayin da ake so a hana sayar mata makamai.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Sanata Bernie Sanders na kasar Amurka ya sanar da cewa zai tabbatar da cewa ya jagoranci hana gwamnatin kasar shi tura makamai Isra'ila.
Sanders ya yi magana ne yayin da ya ke zargin Isra'ila da kisan kare dangi a Gaza, inda ya ce bai kamata Amurka ta taimaka mata ba.
Asali: Legit.ng
