Ali Nuhu Ya Fito Ya Gayawa Duniya Halin da Adam A. Zango Ya Samu Kansa a Ciki

Ali Nuhu Ya Fito Ya Gayawa Duniya Halin da Adam A. Zango Ya Samu Kansa a Ciki

  • An ji daga bakin jarumi Ali Nuhu kan halin da Adam A. Zango ya samu kansa a ciki bayan ya fito ya nuna damuwarsa
  • Shugaban hukumar fina-finan ta Najeriya, ya yi nuni da cewa komai ya daidaita kuma yanzu haka jarumin na cikin ƙoshin lafiya
  • Wallafar da Adam Zango ya yi dai ta sanya masoyansa da abokan aikinsa sun shiga damuwa bayan ya nuna cewa akwai wani abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ali Nuhu ya fito ya yi magana kan halin da jarumin masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya samu kansa a ciki.

Ali Nuhu wanda shi ne shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, ya bayyana cewa Adam A. Zango na cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

"Ina cikin mawuyacin hali": Adam A Zango ya koka kan rashin samun farin ciki a rayuwa

Ali Nuhu ya yi magana kan Adam A. Zango
Ali Nuhu ya ce Adam A. Zango na cikin koshin lafiya Hoto: realalinuhu
Asali: Instagram

Maganar Ali Nuhu na zuwa ne biyo bayan wallafar da fitaccen jarumin ya yi kan cewa yana cikin wani mawuyacin hali a rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hali Adam Zango yake ciki?

A wallafar da Adam A. Zango ya yi a shafinsa na Instagram ya nuna cewa yana cikin damuwa, inda har ya tambaya cewa ko idan ya daina waƙa da fim zai samu kwanciyar hankali.

Sarkin na Kannywood a wani rubutu a shafinsa na Instagram ya bayyana cewa abin da ya faru da jarumin ba komai ba ne face halayya ta ɗan Adam wajen jin haushi a wasu lokutan kan wasu abubuwa da suka faru.

Ya nuna godiyarsa kan yadda masoya suka riƙa nuna damuwa, kulawa da yin addu'o'i kan halin da jarumin ya tsinci kansa a ciki.

A kalamansa:

"Lafiyarsa ƙalau kuma yanzu komai ya daidaita. Wasu lokutan muna jin haushi kan wasu abubuwa saboda mu mutane ne. Muna godiya bisa kulawa, nuna damuwa da addu'o'i. Mun gode matuƙa."

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

Adam Zango yana ganin likita

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Adam A Zango, ya bayyana cewa yana samun kulawar likita kan cutar damuwa da ke damunsa bayan rabuwa da matarsa.

Auren Adam Zango da matarsa Safiyya Umar Chalawa ya zo ƙarshe a watan Afirilun 2023, bayan sun shafe watanni suna fafatawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel