Akpabio: Barazanar Iran a Najeriya Ta Sa Amurka Daukar Mataki a Abuja

Akpabio: Barazanar Iran a Najeriya Ta Sa Amurka Daukar Mataki a Abuja

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Goswill Akpabio ya yi karin haske game da matakin da Amurka ta dauka na janye jami'ai a Najeriya
  • Akpabio ya yi magana ne a matsayin martani kan maganganun da jama'a ke yi na cewa Amurka da wasu kasashe na rage jami'ansu a kasar nan
  • A kwanakin baya ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da janye wasu daga cikin jami'an da ke aiki a ofishin jakadancinta da ke Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Amurka ta rage yawan ma’aikatanta a ofishin jakadancinta da ke Najeriya saboda fargabar yiwuwar hare-hare da ke da alaka da rikicin Iran.

Akpabio ya bayyana haka ne yayin kaddamar da sabuwar hedikwatar Hukumar Ayyukan Majalisar Dokoki ta Kasa a Abuja, inda ya yi tsokaci kan rahotannin cewa wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje na rage ayyukansu a kasar.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad

Sanata Godswill Akpabio a majalisar dattawan Najeriya
Sanata Godswill Akpabio a zauren Majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Dalilin janye jami'an Amurka a Najeriya

A martanin da ya yi, Punch ta walllafa cewa Akpabio ya ce lamarin ba Najeriya kadai ya shafa ba, ya ce wani bangare ne na matakan tsaro na duniya da wasu kasashe ke dauka.

Ya ce:

“Wasu na cewa har yanzu wasu na rufe ofishin jakadancinsu. Kadan ne ke rufewa. Da dama suna tsoron martani daga abokan gaba.”

Ya kara da cewa:

“Misali, zan iya cewa Amurka na dan damuwa da yiwuwar harin bam daga Iran, don haka a fadin duniya suna rage ma’aikatansu idan har Iran ta yanke shawarar kai hari kan ofishin jakadancinsu.”

Akpabio ya karyata zargin cewa wannan lamari yana da alaka da yanayin siyasar Najeriya ko kuma zabuka masu zuwa, yana mai cewa kasashen waje na daukar mataki ne bisa la’akari da tsaron kasa da kasa.

Ya ce:

“Wasu na tunanin cewa ofisoshin jakadanci na rufewa ne saboda zabe na tafe. Ba haka ba ne.”

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi babban matsalar Amurka a shirin yarjejeniyar zaman lafiya

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na sauraron wani jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matakin da Amurka ta dauka a Najeriya

A baya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba da izinin ficewar ma’aikatan gwamnati da ba su muhimmin aiki tare da iyalansu daga ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, tana mai danganta hakan da tabarbarewar tsaro a Najeriya.

A cikin sabon gargadin tafiye-tafiye da aka fitar a makon jiya, ma’aikatar ta ce daga ranar 8 ga Afrilu, 2026, ana shawartar ‘yan Amurka da su sake tunanin zuwa Najeriya saboda matsalolin ta’addanci, da sauransu.

Amurka ta dakatar da bayar da biza a Abuja yayin da ta yi gargadi a kan zuwa wasu jihohin Najeriya da suka hada da Yobe, Benue, Bayelsa da sauransu.

Ga bidiyon Akpabio da tashar Arise ta wallafa a X:

Amurka ta yaba wa Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta yaba wa Najeriya kan gurfanar da 'yan ta'adda da dama da yanke musu hukuncin daurin shekaru.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

Hadimin shugaba Donald Trump mai lura da kasashen Larabawa da Afrika, Massad Boulos ne ya fitar da sanarwar a madadin Amurka.

Massad Boulos ya bayyana cewa za su cigaba da aiki tare da Najeriya wajen ganin kasar ta magance matsalar rashin tsaro da ta yi katutu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng