An Zo Wajen: Akpabio Ya Fasa Kwai, Ya Fallasa Masu Daukar Nauyin Matsalar Rashin Tsaro

An Zo Wajen: Akpabio Ya Fasa Kwai, Ya Fallasa Masu Daukar Nauyin Matsalar Rashin Tsaro

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya dauko batun matsalar rashin tsaro da ake ta fama da ita
  • Sanata Akpabio ya bayyana cewa akwai mutanen da ke daukar nauyin matsalar rashin tsaro domin cimma burikansu na siyasa
  • Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro za ta zo karshe da zarar an kammala zaben shekarar 2027

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan karuwar matsalar rashin tsaro.

Akpabio ya yi zargin cewa karuwar rashin tsaro da ake samu a faɗin Najeriya kwanan nan yana da nasaba da siyasa da kuma babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Akpabio ya fadi masu ruwa wutar tashin tsaro
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, a zaman majalisa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026 yayin jawabin taya murna a wajen kaddamar da babban ofishin hukumar tara kudaden shiga ta ƙasa (NRS).

Kara karanta wannan

Malamin addinin Musulunci ya shiga takarar gwamnan Zamfara, ya zabi jam'iyya

Me Akpabio ya ce kan rashin tsaro?

Ya bayyana cewa wasu ’yan siyasa ne ke ɗaukar nauyin tashe-tashen hankula domin dakile damar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

“Kuna ganin rashin tsaro a yau, har ma ƙaruwa yake yi saboda zaɓe na gabatowa. Da zaran an gama zaɓe, a cikin makonni biyu na farko ba za ku sake jin ƙarar bam ko guda ɗaya ba."
"Domin mutane ne ke ɗaukar nauyin hakan don shagaltar da ku; ba su san abin da za su yi ba, sai su ce wannan mutumin (Tinubu) yana da ƙwarewa sosai a fannoni da dama.”

- Godswill Akpabio

Akpabio ya yi maganar farin jinin Tinubu

Ya yi nuni da abin da ya kira ƙaruwar goyon baya na siyasa da shugaban ƙasar ke samu, inda ya nuna cewa gwamnoni da dama sun dawo ƙarƙashin inuwar Tinubu tun bayan 2023, jaridar Daily Trust ta dauko rahoton.

“Gwamnoni suna son sa ne saboda yana kula da jihohinsu sosai. Ya shigo da gwamnoni 18, amma a yau yana da kusan gwamnoni 32 a ƙarƙashinsa cikin 36. Don haka, a ina muke?”

Kara karanta wannan

Ana barazanar hana ADC taro a Abuja, Atiku ya fadi matakin da za su dauka

- Godswill Akpabio

Shugaban majalisa ya soki 'yan adawa

Ya kuma yi magana game da takaddamar da ta shafi wani shafin X da ake zargin shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, ne ke amfani da shi, inda ya yi watsi da zargin nuna son kai a harkar zaɓe.

“Yaya za ku ci zaɓe alhalin ba ku da tsari? Babu wata jam’iyyar siyasa da take zaune lafiya a ƙasar nan. Sai su sauya sheka su koma suna sukar mutanen da za su gudanar da zabe."
"Sai suka fito da wani saƙon X inda shugaban INEC ya ce, ‘Nasara tana nan tabbas,’ amma bai ce nasarar ta APC ce ko ta PDP ba."

- Godswill Akpabio

Akpabio ya yi magana kan rashin tsaro
Sanata Godswill Akpabio a zauren majalisa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Wannan bayani na Akpabio na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar fargaba kan tsaro a faɗin ƙasar, biyo bayan jerin tashe-tashen hankula da suka faru a kwanakin nan.

'Yan Boko Haram sun kashe babban kwamanda

Kara karanta wannan

'Sai dai a mutu,' Kasar Cuba ta daina jin tsoron Trump, ta shirya yaki da Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun hallaka dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun hallaka babban jami’i a sojojin Najeriya, mai suna Kanar I.A. Muhammad, tare da wasu sojoji shida.

Majiyoyi sun bayyana cewa babban jami’in ya rasa ransa yayin da yake jagorantar tawagar kai ɗauki domin fatattakar ’yan ta’addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng