Gwamnatin Borno Ta Sha Alwashin Ceto Ragowar 'Yan Matan Chibok da Ke Hannun Boko Haram

Gwamnatin Borno Ta Sha Alwashin Ceto Ragowar 'Yan Matan Chibok da Ke Hannun Boko Haram

  • Gwamnatin jihar Borno ta yi magana kan ragowar ƴan matan Chibok da har yanzu suke tsare a hannun Boko Haram
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce gwamnatin ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin sauran ɗaliban sun kuɓuta
  • Ya yi nuni da gwamnatin ba za ta taɓa wasa da rantsuwar da ta yi ba wajen ganin cewa ɗaliban sun dawo wajen iyalansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa ta haɗa kai da jami’an tsaro domin ceto sauran ƴan matan Chibok 89 bayan shafe shekara 10 a hannun ƴan Boko Haram.

Kwamishinan yaɗa labarai da tsaro na cikin gida, Farfesa Usman Tar, shi ne ya bayyana hakan a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Kungiya ta ja kunnen Gwamna Abba kan binciken Ganduje, an ba shi shawarar abin da ya kamata ya yi

Gwamnatin Borno za ta ceto 'yan matan Chibok
Gwamnatin Borno na shirin ceto 'yan matan Chibok da ke tsare Hoto: @govborno
Asali: Facebook

Kwamishinan ya ce tare da taimakon jami'an tsaro, hukumomin leƙen asiri da al'umma, dukkanin ƴan matan Chibok da aka ɗauke za su dawo, rahoton jaridar Gazettengr ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane ƙoƙari ake don ceto ƴan matan Chibok?

A cewarsa, gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da rantsuwar da ta yi ba kan cewa dukkanin ƴan matan Chibok sai sun dawo gida wajen iyalansu.

Ya bayyana cewa a baya-bayan nan jami’an tsaro sun kuɓutar da ƴan matan Chibok 16, kuma tuni gwamnatin jihar ta fara ba su kulawa domin samun rayuwa mai inganci.

A kalamansa:

"A wannnan rana ta cika shekara 10 da sace ƴan matan Chibok, gwamnatin jiha tana sanar da jama'a cewa za mu ci gaba da ƙoƙarin ceto ƴan matanmu a madadin iyaye da ƴan'uwa na ƴan matan Chibok da har yanzu suke a tsare."

Kara karanta wannan

'Yan daba 200 sun tuba, sun zama nagari, inji Gwamnan Kano

"Gwamnatin Borno ta mayar da hankali wajen ceto sauran ƴan matan Chibok tare da sada su da iyalansu. Mun fahimci bakin ciki da ƙunar da iyalan sauran ɗaliban suke ciki, wannan baƙin cikin na mu ne gabaɗaya."
"Ya zuwa yanzu, daga cikin ƴan matan Chibok 276 da aka sace, an ceto ɗalibai 187 tare da sada su da iyalansu."

Sojoji sun yi kamu a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun cafke aƙalla mutum shida masu yi wa ƴan ta'addan Boko Haram safarar kayayyaki a jihar Borno.

Sojojin sun cafke ɓata garin ne tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro a ranar Asabar, 13 ga watan Afirilun 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel