Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu bata garin mutane wadanda ke yi wa 'yan ta'addan Boko Haram safarar kayayyaki a jihar Borno.
Wata babbar kotu mai zamanta a jihar Kano, ta haramtawa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano daga dakatar da wasu kamfanoni guda uku na Kannywood.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon manajan daraktan kamfanin FHAEDL. Injiniya Kabir Musa Umar shi ne aka nada a wannan mukamin a kamfanin.
Wani dan aike ya fallasa yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, yake sanya shi yana karbo masa Daloli a gaban kotu da ke Legas.
Karamin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle, ya yaba sojojin Najeriya kan nasarorin da suke samu na sheke 'yan ta'adda. Ya ce za su kawo karshen matsalar.
An fafata a tsakanin mayakan kungiyoyin ta'addanci na ISWAP da Boko Haram. Kazamin fadan da 'yan ta'addan suka fafata ya jawo an kashe tsageru masu yawa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sakon ta'aziyya kan rasuwar shahararriyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso. Ya ce an yi babban rashi.
Ana zargin jami'an hukumar NSCDC da hallaka wata mata a filin Idi a jihar Zamfara. Jami'an 'yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano gaskiya kan lamarin.
Tsohon alkalin kotun daukaka, Ahmad Olarewaju Belgore, ya yi bankwana da duniya yana da shekara 71. An bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari