Gwamna Radda Ya Fadi Babban Alkawarin da Cikawa Al'ummar Jihar Katsina

Gwamna Radda Ya Fadi Babban Alkawarin da Cikawa Al'ummar Jihar Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya yi magana kan alƙawuran da ya ɗaukarwa mutanen jihar Katsina
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa cikim watanni takwas ya cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe
  • A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labaran jihar, an jero nasarorin da Gwamna Radda ya samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umar Radda na Katsina ya ce ya cika alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓensa.

Gwamnan ya ce a cikin watanni takwas da ya kwashe kan kujerar mulki, ya cika alƙawuran da ya yi wa al'ummar Katsina, cewar rahoton jaridar The Nation.

Gwamna Radda ya cika alkawura
Gwamna Radda ya ce ya cika alkawuran da ya yi wa Katsinawa Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa wacce ke ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labaran jihar Katsina, Bala Salisu Zango.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta sha alwashin ceto ragowar 'yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dikko ya kuma yi alƙawarin ci gaba da samar da abubuwan more rayuwa a jihar Katsina..

Waɗanne alƙawura Gwamna Radda ya cika?

Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin alƙawuran da ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe waɗanda ya cika sun haɗa da tsaro, ilimi, samar da ruwan sha, kiwon lafiya, sake fasalin hukumomi da dai sauransu.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Gwamnatina ta ɗauki malamai 7,325, ta ba ƴan asalin jihar Katsina guraben karatu a ƙasashen waje don yin karatun likitanci a Masar, ta sayo takin zamani domin noman damina."
"Gwamnati ta rabawa marasa galihu tallafi, sayan magunguna da kayan aikin asibiti, gyara cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar da ɗaga darajar ƙananan asibitoci biyu matakin babban asibiti da dai sauransu."

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Katsina, mai suna Jamilu Abubakar, wanda ya yaba da ƙokarin da gwamnan ya yi a ƴan watanni da ya kwashe kan mulki.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Jamilu ya bayyana cewa Gwamna Radda ya yi ƙoƙari sosai amma batun cewa ya cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka, akwai sake a cikinsa.

A kalamansa:

"Eh ya yi ƙoƙari sosai amma batun cewa ya cika alƙawuran da ya ɗauka ba haka abin yake ba. Ya yi ƙoƙari ta ɓangare tsaro amma har yanzu akwai sauran aiki."
"Ya ɗauki malaman makaranta kuma yanzu haka ana tantance malaman kiwon llafiya da za a ɗauka aiki."

Gwamna Radda ya musanta ciyo bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya musanta rahoton ofishin kula da basussuka (DMO) na cewa yana cikin gwamnonin da suka karɓo sabon bashi.

Gwamnan ya jaddada cewa tun da gwamnatinsa ta fara mulki a Katsina take biyan basussukan da ta gada daga gwamnatocin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel