Manyan Labarai A Yau
Jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya nuna cewa kasarsa ba za ta nuna tausayi ba a yakin da take yi da haramtacciyar gwamnatin Isra'ila.
Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta fito ta nesanta kanra daga batun cewa ta marawa Nuhu Ribadu baya don neman wani mukamin siyasa a zaben 2027.
Babban kusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Ismaeel Ahmed, ya musanta cewa akwai wani sabani a tsakanin shugaban kasa Bola Tinubu da Ƙashim Shettima.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikƙo Umaru Radda ya samu lambara yabo ta gwamna mafi aiki a shekarar 2025, an yaba masa bisa yadda yake kawo ci gaba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa sun san inda jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Khamenei, yake boye. Ya ce ba za a kashe shi ba.
Gwamnatin jihar Benue ta ba da hutu domin ziyarar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai jihar. Ta ce ziyarar na da matukar muhimmanci sosai.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun hallaka mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu zuwa daji.
Rasha ta kai hari mai tsanani kan Kyiv, inda ta kashe mutane 15. Shugaba Zelenskyy ya kira harin da mafi muni yayin da ya nemi kasashen duniya su ce wani abu.
Tankokin yakin Isra'ila sun bude wuta kan Falasdinawan da suka je wurin karbar abinci a zirin Gaza. An samu asarar rayuka sakamakon wutar da sojoji suka bude.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari