Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Neja Ta Bayyana Adadin Mutanen da Suka Bace

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Neja Ta Bayyana Adadin Mutanen da Suka Bace

  • Gwamnatin jihar ta yi magana kan irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi a garin Mokwa a ƴan kwanakin baya
  • Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa har yanzu akwai mutane fiye da 700 da suka ɓace waɗanda ake nema
  • Ya nuna ambaliyar ruwan ta jawo rugujewar gidage masu yawa wanda hakan ya tilastawa mutane rasa matsugunansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja ta ƙara fitar da bayanai kan ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi a Mokwa.

Gwamnatin ta bayyana cewa sama da mutane 700 ne har yanzu ba a gano inda suke ba sakamakon ambaliyar da ta faru a Mokwa da ke cikin ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Neja
Gwamnatin Neja ta ce mutane 700 sun bace sakamakon ambaliyar ruwa Hoto: Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Gwamna Umaru Bago na Neja ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin tsohon dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, da abokansa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar Hamza Al-Mustapha ta je ziyara ta’aziyya ne ga gwamnan dangane da ambaliyar da ta faru a Minna a ranar Talata.

Me gwamnatin Neja ta ce kan ambaliyar ruwa?

Gwamnan, wanda mataimakinsa, Yakubu Garba, ya wakilta, ya kuma bayyana cewa mutane 207 ne aka tabbatar sun mutu, yayin da fiye da mutane 3,000 suka rasa matsugunansu.

"Har yanzu ba a san inda fiye da mutane 700 suke ba. Ambaliyar ta haddasa mummunan ɓarna."

- Gwamna Umaru Bago

Ya ƙara da cewa ambaliyar ta lalata gidaje 400, inda gidaje 283 da shaguna 50 suka ruguje gaba ɗaya.

Gwamna Bago ya nuna godiyarsa ga mutane da ƙungiyoyin kamfanoni masu zaman kansu bisa gudunmawar da suka bayar, yana mai cewa wannan lamari annoba ce ta ƙasa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki tare da ƙwararrun masana domin gano musabbabin ambaliyar, kuma suna jiran sakamakon binciken da ake gudanarwa.

Al-Mustapha ya jajantawa mutanen Neja

Tun da farko, Al-Mustapha ya bayyana cewa ziyararsu na da nufin jajantawa gwamnatin jihar Neja da al’ummar Mokwa bisa iftila’in ambaliya da ya shafi yankin.

Gwamnatin Neja ta yi bayani kan ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa ta yi barna a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original
“Mun zo ne domin miƙa saƙon ta’aziyya bisa ambaliyar da ta auku a Mokwa, duba da irin asarar da aka yi da yadda ta shafi jihar."
"Za mu gana da majalisar sarakunan gargajiya, musamman shugaban gargajiya na Mokwa, kuma mu yi addu’ar don neman rashin sake aukuwar irin wannan lamarin."

- Hamza Al-Mustapha

Al-Mustapha ya bayyana cewa tawagarsu ta ƙunshi manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan, waɗanda suka zo domin nuna goyon baya da jajantawa ga gwamnatin jihar da al’ummar da lamarin ya shafa.

Gwamna Zulum ya ba da tallafi a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Neja.

Gwamna Zulum ya ba da tallafin N300m domin rabawa ga mutanen da mummunan lamarin ya ritsa sa su.

Gwamnatin jihar Neja ta yabawa Zulum kan gudunmawar da ya ba da, inda ta yi alƙawarin cewa za a yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng