"Ana Kokarin Kirkirar Rigima": Jigo a APC Ya Magantu kan Sabani tsakanin Tinubu, Shettima
- Babban kusa a jam'iyyar APC ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa dangantakanta yi tsami tsakanin Bola Tinubu da Kashim Shettima
- Ismaeel Ahmed wanda babban 'dan siyasa ne ya musanta cewa akwai shiri da ake yi don sauya Shettima kafin babban zaɓen 2027
- Tsohon jagoran na matasa ya nuna cewa babu wata ɓaraka a tsakanin shugabannin biyu kuma jita-jitar babu komai a cikinta face ƙarya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigo a jam’iyyar APC, Ismaeel Ahmed, ya yi magana kan jita-jitar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sauya Kashim Shettima kafin zaɓe mai zuwa.
Ismaeel Ahmed ya yi watsi da jita-jitar wadda ke cewa akwai wani shiri da ake yi na maye gurbin mataimakin shugaban ƙasan a zaɓen shekarar 2027.

Asali: Facebook
Jigon na APC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a daren Talata, 17 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mamban na kwamitin amintattu na jam’iyyar APC ya bayyana wannan zargi a matsayin “muguwar jita-jita” tare da jaddada cewa babu wani abu da ke nuna cewa akwai saɓani tsakanin shugabannin biyu.
"Wannan batun (na saɓani) ba gaskiya ba ne. Na san hakan sosai. Wane ne yake da kaso 100% cikin 100% na daidaito da wani? Akwai yarda tsakanin Shugaba Tinubu da Shettima. Muna ƙoƙarin ƙirƙirar matsala ne inda babu ita."
“Duk wannan magana, a ganina, jita-jita ce kawai, jita-jita ce kawai tsantsa. Ina da tabbacin cewa babu wata tattaunawa da ake yi kan sauya mataimakin shugaban ƙasa."
"Babu wata magana da ake yi kan cewa an hana mataimakin shugaban ƙasa yin aikinsa."
"Waɗannan duka jita-jita ce daga mutanen da ko dai ba su fahimci abubuwan da ke faruwa a fadar shugaban ƙasa ba, ko kuma ba su san yadda fadar shugaban ƙasa ke aiki ba."
- Ismaeel Ahmed
An ba ƴan jam'iyyar APC shawara
Ismaeel Ahmed ya buƙaci mambobin jam’iyyar APC da kuma ƴan Najeriya su mayar da hankali kan mulki, maimakon barkwanci da hayaniyar siyasa.
Ya bayyana cewa har yanzu gwamnati na da manyan ayyuka da ya kamata ta kammala waɗanda ta yi alƙawarin a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Asali: Twitter
"Muna da nauyin jama'a na shekaru huɗu. Shekaru biyu sun wuce, saura shekara guda zuwa zaɓukan fidda gwanin jam’iyya, da kuma shekaru biyu zuwa babban zaɓe."
"Don Allah, muna cikin gwamnati, kuma muna cikin jam’iyyar da ke mulki. Wannan yana nufin dole ne aƙalla mu kiyaye dokokin hukumar zaɓe ta INEC. Mu maida hankali wajen gudanar da mulki."
- Ismaeel Ahmed
Sule Lamido ya soki Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki Sbugaba Bola Tinubu.
Sule Lamido ya zargin shugaban ƙasan da ƙoƙarin sauya tarihin gwagwarmaya kan rsnar 12 ga watan Yunin 1992.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa jawabin da shugaban ƙasan a bikin ranar dimokuraɗiyya, wani yunƙuri ke na karkatar da tarihi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng