Wata Sabuwa: Trump Ya Yi Maganar Yiwuwar Kashe Shugaban Iran, Ayatollah Khamenei

Wata Sabuwa: Trump Ya Yi Maganar Yiwuwar Kashe Shugaban Iran, Ayatollah Khamenei

  • Shugaban ƙasan Amurka, Donald Trump, ya sake yi kalaman kan jagoran ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei
  • Mista Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta san inda jagoran juyin juya halin yake ɓoye a halin yanzu
  • Hakazalika ya Trump ya buƙaci Iran da ta miƙa wuya ba tare da sa wani sharaɗi ba a yaƙin da take yi da ƙasar Isra'ila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kasar Amurka - Shugaban ƙasan Amurka, Donald Trump, ya ƙara tsananta kalamansa kan jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Donald Trump mai shekara 79 a duniya ya bayyana cewa Amurka ta san inda Khamenei yake ɓoye.

Trump ya ce ba za a kashe Khamenei ba
Trump ya tabo batun kashe Khamenei Hoto: @RealDonaldTrump, @Khamenei_ir
Asali: Getty Images

Jaridar Sky News ta rahoto cewa shugaban na ƙasar Amurka ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Donald Trump ya ce kan Ayatollah Khamenei?

Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta san inda Khamenei yake ɓoye, amma ba za su kashe shi ba a yanzu, rahoton Reuters ya tabbatar da hakan.

A wani saƙo na daban, Trump ya bayyana cewa yana buƙatar “Miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba!" daga Iran.

Kalamansa sun ƙara nuna alamomin tambayoyi kan yiwuwar shigar Amurka cikin harin da Isra’ila ke kaiwa kan shugabannin Tehran da kuma wuraren nukiliyarta.

"Mun san haƙiƙanin inda wannan da ake kira jagora yake ɓoye. Za a iya kai masa hari cikin sauƙi amma yana cikin aminci a inda yake. Ba za mu kashe shi ba (aƙalla ba yanzu ba)."
"Amma ba ma so a harba makamai masu linzami kan fararen hula ko sojojin Amurka. Haƙurinmu na ƙarewa. Na gode da kulawarku a wannan al’amari!"

- Donald Trump

Cikin ƴan mintoci kaɗan bayan haka, shugaban na Amurka ya sake wallafa wani saƙo kai tsaye da cewa: “Miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba!"

Donald Trump ya baro taron G7

Trump ya dawo daga taron G7 da aka gudanar a Kanada da wuri a daren Litinin, yayinda rikici ke ƙara tsananta tsakanin Iran da abokiyar hamayyarta Isra’ila.

Donald Trump ya dawo daga taron G7
Trump ya ce Amurka ba za ta kashe Khamenei ba Hoto: @RealDonaldTrump
Asali: Getty Images

An shirya shugaban ƙasan zai gana da manyan jami’an tsaro a dakin taron gaggawa na Fadar White House a ranar Talata.

Ya zuwa yanzu, Trump ya jaddada cewa Amurka ba ta da niyyar shiga wannan rikici kai tsaye, kuma ya ce Iran har yanzu na da damar karɓar yarjejeniyar da ya gabatar kafin Isra’ila ta fara kai hare-hare.

Sai dai alamu na ƙara nuna cewa Amurka na iya shiga cikin rikicin nan gaba kaɗan ta wata hanya.

China ta nuna yatsa ga Trump

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa China ta nuna yatsa ga Donald Trump kan yaƙin da ake yi tsakanin ƙasashen Iran da Isra'ila.

China ta zargi Donald Trump ta ingiza wutar rikicin da ake yi tsakanin ƙasashen guda biyu waɗanda ba sa ga maciji da juna.

Zargin ƙasar China na zuwa ne bayan shugaban ƙasan na Amurka ya buƙaci mazauna Tehran da su fice daga birnin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng