Gwamnatin Benue Ta Ayyana Ranar Hutu don Ziyarar Bola Tinubu

Gwamnatin Benue Ta Ayyana Ranar Hutu don Ziyarar Bola Tinubu

  • Gwamnatin jihar Benue ta shirya tarbar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ziyarar da zai kai zuwa a tsakiyar makon nan
  • Ta ayyana ranar Laraba a matsayin lokacin hutu ga ma'aikata a faɗin jihar saboda ziyarar da shugaban ƙasan zai kawo
  • Sakatariyar gwamnatin jihar ta buƙaci dukkanin mutane da su fito domin tarbar mai girma Bola Tinubu da tawagarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ta ayyana ranar hutu domin ziyarar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kai a jihar.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Hyacinth Alia ta ayyana ranar Laraba, 18 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a faɗin jihar.

Gwamnatin Benue ta ayyana ranar hutu
Gwamnatin Benue ta ba da hutu saboda ziyarar Bola Tinubu Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Deborah Aber, ta fitar a ranar Talata a birnin Makurdi, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnatin Benue ta ba da hutu?

Ta bayyana cewa an ba da hutun ne domin girmama ziyarar da shugaban ƙasan zai kai a jihar, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

"An ayyana wannan ranar hutun ne domin girmama zuwan shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunonin sojojin ƙasar nan, Bola Ahmed Tinubu, wanda zai kai ziyara ta yini guda zuwa jihar Benue."
“Ziyarar tana da nufin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Benue dangane da matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar jihar."

- Deborah Aber

Deborah Aber ta buƙaci al’ummar jihar da su fito kwansu da ƙwarƙwatarsu domin tarbar Shugaba Tinubu da tawagarsa yayin ziyarar.

Gwamnatin jihar ta ce wannan ziyara na da matuƙar muhimmanci, saboda haka za a buƙaci haɗin kan jama’a wajen tarbar shugaban ƙasa.

Shugaba Tinubu zai je jihar Benue

A ranar Litinin, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai kai ziyara zuwa jihar Benue a ranar Laraba.

Shugaban ƙasan zai kai ziyarar ne a wani mataki na ƙara ƙarfafa yunkurin samar da zaman lafiya da magance rikice-rikicen da suka dade suna addabar al’ummomin jihar.

Shugaba Tinubu zai ziyarci Benue
Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar Benue Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Hakazalika, an ɗage ziyarar da shugaban ƙasa ya shirya kai wa jihar Kaduna, wadda a baya aka tsara zai kai a ranar Laraba domin ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya shirya kai ziyara zuwa jihar Kaduna a ranar Laraba domin buɗe wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta kammala.

Sai dai sakamakon muhimmancin ziyararsa zuwa jihar Benue dangane da matsalar tsaro da ta addabi al’ummar jihar, an ɗage ziyarar Kaduna zuwa wani lokaci.

Peter Obi ya yabi Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu.

Peter Obi ya yabawa shugaban ƙasan ne kan shirinsa na kai ziyara zuwa jihar Benue biyo bayan hare-haren ƴan bindiga.

Hakazalika Obi ya buƙaci shugaban ƙasan da ya kai irin wannan ziyarar zuwa jihar Neja domin jajantawa mutane kan ambaliyar ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng