Hare Haren 'Yan Bindiga: Shugaba Bola Tinubu Ya Isa Jihar Benue

Hare Haren 'Yan Bindiga: Shugaba Bola Tinubu Ya Isa Jihar Benue

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Makurdi na jihar Benue yayin ziyarar da ya kai
  • Mai girma Tinubu ya ziyarci jihar Benue ne domin jajantawa kan munanan hare-haren da ƴan bindiga suke kai wa
  • A yayin ziyarar ta sa, Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki don nemo mafita kan hanyoyin kawo ƙarshen rikicin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Jirgin Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Shugaban ƙasan ya isa birnin ne a daidai lokacin da yake shirin kai ziyara zuwa ƙauyen Yelwata da ke cikin ƙaramar hukumar Guma ta jihar Benue.

Shugaba Tinubu ya isa jihar Benue
Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Benue Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta ce Shugaba Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Makurdi da ke cikin sansanin rundunar sojin saman Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya sauka a Benue

Shugaban ƙasan ya ya iso filin jirgin saman ne da misalin ƙarfe 12:58 na rana a ranar Laraba.

Ana sa ran shugaban ƙasan zai gana da manyan masu ruwa da tsaki dangane da hare-haren da suka yi sanadiyya rasa rayuka da dama a wasu sassan jihar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Gwamnatin jihar ta ba da hutu a ranar ziyarar domin tarbar shugaban ƙasa.

Ana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai gana da iyalan waɗanda rikicin ya shafa, waɗanda suka rasa matsugunansu, waɗanda suka jikkata, da kuma shugabannin al’umma da rikicin ya shafa kai tsaye.

Tinubu zai yi taro a jihar Benue

Haka zalika, ana sa ran zai gana da shugabannin siyasa, na addini, da na gargajiya a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar Benue da ke Makurdi, inda zai jagoranci babban taron tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki.

Wannan taro wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi domin samo mafita ta dindindin ga rikicin da ya shafi wasu sassan jihar, musamman yankunan karkara.

Ana sa ran manyan jami’an gwamnati na jiha da na ƙasa za su halarci taron, ciki har da gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia da gwamnonin wasu jihohin ƙasar, musamman na yankin Arewa ta Tsakiya, Nuhu Ribadu da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Shugaba Bola Tinubu ya isa jihar Benue
Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hakanan, manyan hafsoshin tsaro, mambobin majalisar tarayya, shugabannin jam’iyyar APC mai mulki, da wasu fitattun mutane musamman waɗanda ke wakiltar yankunan da rikicin ya fi shafa a Benue za su halarci taron.

Sauran baƙi masu muhimmanci sun haɗa da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar APC (NWC), da mambobin majalisar tarayya, musamman waɗanda ke wakiltar al’ummomin da rikicin ya fi shafa a jihar Benue

Sarakunan gargajiya daga ƙabilu daban-daban na jihar suma ana sa ran za su halarci taron, kasancewar suna da muhimmiyar rawa wajen warware rikice-rikice da haɗa kai da al’umma.

Shugabannin ƙananan hukumomi 23 da ke cikin jihar, mambobin majalisar dattawan daga Benue, da kuma mambobin majalisar dokokin jihar suma ana sa ran za su halarci wannan muhimmin taro.

Gwamnan Benue ya fallasa masu kai hare-hare

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana mutanen da ke kai harin ta'addanci a jihar.

Gwamna Alia ya bayyana cewa makiyaya masu ɗauke da makamai waɗanda ba su da shanu ne ke kai hare-hare a jihar.

Hyacinth Alia ya nuna cewa mafi yawan makiyayan baƙin haure ne domin ba ƴan asalin jihar Benue ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng