Manyan Labarai A Yau
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko waye ba sun tare hanya a jihar Benue. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da fasinjojin da ke kan hanyar zuwa birnin Makurdi.
Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa abin fashewa na UXO ne ya tarwatse a cikin kayan ƴan gwangwan a Kano, ba bam ba ne kamar yadda mutane ke yaɗawa.
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi karin kudi kan yadda yake sayar da litar fetur. Karin farashin fetur ya fara aiki ne daga ranar daga ranar Litinin.
Mutane biyu sun mutu a Kano saboda shakar guba a masai yayin da suke kokarin ciro waya. Wannan ba sabon abu bane; an taɓa samun irin wannan lamari a baya.
An samu asarar rayukan wasu shanu a jihar Ogun bayan an tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya. Tsawa da walkiya sun yi sanadiyyar mutuwar shanun.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana aniyarsa ya ganin cewa mai girma Bola Tinubu ya rabu da mulki a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya fito ya nesanta kansa daga batun neman kujerar mataimakin shugaban kasa a 2027.
Rundunar 'yan sandan jihar Plateau ta samu nasarar cafke wasu da ake zarginda hannu kan kisan da aka yi wa masu zuwa daurin aure daga Kaduna zuwa jihar.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun samu nasarar yin raga-raga da 'yan bindiga bayan sun kai wani hari. Sun ceto wasu manoma da aka sace.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari