Iran Ta Kaddamar da Harin Ramuwar Gayya kan Amurka

Iran Ta Kaddamar da Harin Ramuwar Gayya kan Amurka

  • Iran ta kai harin ramuwar gayya kan sansanin sojojin Amurka da ke ƙasar Qatar a yankin Gabas ta Tsakiya
  • An ƙaddamar da kai harin ne kan sansanin sojojin sama na Amurka a daren ranar Litinin 23 ga watan Yunin 2025
  • Iran ta kai harin ne matsayin martani kan farmakin da Amurka ta kai a tashoshin nukiliyarta da zummar lalata su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Gabas ta Tsakiya - Iran ta ƙaddamar da harin makami mai linzami kan wani sansanin sojojin saman Amurka da ke ƙasar Qatar.

Ƙasar Iran ta kai harin a matsayin ramuwar gayya bisa hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyarta.

Iran ta kai hari kan sojojin Amurka
Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tashar AP News ta rahoto cewa Iran ta ƙaddamar da harin ne a ranar Litinin, 23 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iran ta kai hari kan sansanin sojojin Amurka

An bayyana hakan ne a gidan talabijin na gwamnati yayin da ake kunna waƙar soja.

Wani rubutu a allon talabijin ya bayyana harin da cewa 'martani mai ƙarfi kuma mai nasara daga rundunar sojojin Iran kan cin zarafin da Amurka ta yi.'

Harin da aka kai a sansanin sojoji na Al Udeid ya auku ne jim kaɗan bayan Qatar ta rufe sararin samaniyarta a matsayin matakin kariya saboda barazanar da Iran ke yi.

Ƙarar fashewar makami ya girgiza Qatar da daren ranar Litinin, yayin da shaidu suka bayyana cewa sun ga abin da suka bayyana a matsayin makamai masu linzami a sararin samaniyar ƙasar.

Babu wata sanarwa kai tsaye daga hukumomin Qatar dangane da yiyuwar harin a lokacin.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Qatar ta rufe sararin samaniyarta saboda barazanar da Iran ke yi na ɗaukar matakin ramuwar gayya kan Amurka bisa harin da ta kai kan wasu cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran da safiyar Lahadi.

Shugaban kasar Iran ya yi gargaɗi

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya rubuta a shafinsa na X jim kaɗan kafin harin da cewa ƙasarsa za ta maida martani idan aka taɓa ta.

Iran ta farmaki sansanin sojojin Amurka
Iran ta kaddamar da hari kan sansanin sojojin Amurka Hoto: @drpezeshkian
Asali: Getty Images
"Ba mu fara yaƙi ba kuma ba ma neman yaƙi. Amma ba za mu bar hare-hare a kan babbar ƙasar Iran ba tare da martani ba."
"Da dukkan ƙarfinmu, za mu tsaya tsayin daka wajen kare tsaron wannan ƙasa da muke ƙauna, kuma za mu mayar da martani kan kowanne rauni da aka yi wa jikin Iran ta hanyar imani, hikima da ƙuduri. Ya jama'a! Allah ne zai kare mu."

- Masoud Pezeshkian

Ƙasashe na shirin ba Iran makamin nukiliya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Rasha ta bayyana cewa akwai ƙasashen da suka nuna a shirye suke don ba Iran makamin nukiliya.

Dimitry Medvedev wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar tsaron Rasha ya bayyana cewa ƙasashe da dama sun dawo tsagin Iran bayan harin da Amurka ta kai mata.

Ya bayyana cewa akwai wasu ƙasashe da suka nuna a shirye suke su ba Iran makamin nukiliya kai tsaye don kare kanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng