Yaki zai Dawo Sabo: Isra'ila Ta Ce za Ta Cigaba da kai Hari Iran bayan Tsagaita Wuta
- Isra’ila ta ce za ta fara kai hari Tehran sa’o’i kaɗan bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana
- Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce Iran ta karya yarjejeniyar da aka cimma ta hanyar harba makamai, lamarin da Iran ta musanta
- Hakan na zuwa ne bayan Benjamin Netanyahu ya ce Isra’ila ta cimma manufofinta na ragargazar shirin nukiliyar Iran da ingantattun makamanta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Israel - Akwai alamar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Iran ta mutu murus.
Hakan na zuwa ne bayan Isra’ila ta bayyana cewa tana shirin kai hare-hare a tsakiyar birnin Tehran a matsayin martani ga abinda ta kira karya yarjejeniyar da Iran ta yi.

Asali: Twitter
Reuters ta rahoto cewa Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ne ya bayyana hakan a ranar Talata cewa ya bayar da umarni ga sojojin kasar su kai farmaki kan manyan cibiyoyin gwamnatin Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isra’ila ta ce Iran ta karya yarjejeniya
Sa’o’i kaɗan bayan shugaba Donald Trump ya ce tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu ya fara aiki, yana mai rokon bangarorin da kada su karya yarjejeniyar Isra'ila ta fitar da sanarwa.
Sky News ta rahoto Katz ya ce:
"Bisa karya yarjenniyar tsagaita wuta da Iran ta yi, na umurci rundunoninmu su ci gaba da kai hare-haren da suka fi karfi kan kadarorin gwamnati da cibiyoyin ta’addanci a Tehran."
Ya kara da cewa Iran ta nuna rashin girmama yarjejeniyar da shugaban Amurka ya sanar, kuma hakan ya nuna rashin niyyar kawo karshen rikicin da ya shafe kwanaki 12 yana gudana.
Tun da fari, shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Isra’ila ta cimma burinta na kai farmaki Iran, wanda ya hada da lalata shirin nukiliyar Iran da rage karfin makaman ta.
Iran ta musanta kai hari ko karya yarjejeniya
Sai dai gwamnatin Iran ta musanta zargin da Isra’ila ke yi cewa an sake harba makamai zuwa kasarta bayan kiran zaman lafiya.
Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar ya bayyana cewa babu wani hari da suka kai kan Isra’ila tun bayan sanar da tsagaita wuta.
A cewar hukumomin Tehran, an dauki matakin dakatar da duk wata musayar wuta tun lokacin da shugaban Amurka ya sanar da yarjejeniyar, kuma suna ci gaba da kiyaye hakan.

Asali: Getty Images
Iran ta kuma jaddada cewa shirin nukiliyarta na da nufin samar da makamashi da kuma ayyukan lafiya, ba wai kera makaman nukiliya ba kamar yadda Isra’ila ke zargi.
Iran ta yaba wa sojojinta bayan yaki da Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta yaba da sojojinta bisa jarumtar da suka nuna a kwankin da suka shafe suna yaki da Isra'ila.
Gwamnatin Iran ta ce sojojin sun taka rawar gani bisa yadda suka jajirce wajen kare kasarsu daga hare hare na kwanaki 12.
Iran ta yi magana ne bayan amincewa da tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a daren ranar Talata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng