Ana Jimanin Kisan 'Yan Daurin Aure, 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji

Ana Jimanin Kisan 'Yan Daurin Aure, 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare wata mota mallakin kamfanin sufuri na jihar Benue wadda ta ɗauko fasinjoji
  • A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa motar ta taso ne daga birnin Abeokuta zuwa Makurdi inda aka tare ta cikin jihar Benue
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ta tura jami'ai domin ƙoƙarin ceto fasinjojin da aka sace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Hukumar gudanarwar kamfanin sufuri na jihar Benue ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun tare ɗaya daga cikin motocinsu.

Kamfanin wanda aka fi sani da Benue Links Limited ya ce an tare motar ne da ke tafiya daga Abeokuta zuwa Makurdi a yammacin ranar Lahadi a jihar Benue.

'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Benue
'Yan bindiga sun tare motar fasinjoji a Benue Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Johnson Daniel, ya fitar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace fasinjoji a Benue

Ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a yankin Eke Elengbecho da ke ƙaramar hukumar Okpokwu, rahoton The Punch ya tabbatar da zancen.

Sanarwar ta ce, motar wacce ke ɗauke da kujeru 14, mai lambar rajista 14B-143BN, ta bar Abeokuta da fasinjoji 12 da direba kafin ƴan bindiga su kai musu hari.

“An gano motar daga baya a gefen hanya a Eke tare da wasu daga cikin kayayyakin fasinjoji, amma direban da fasinjoji 11 ba a gan su ba."

- Johnson Daniel

Sanarwar ta ƙara da cewa, ɗaya daga cikin fasinjojin ya samu nasarar tserewa, kuma ya kai rahoton lamarin zuwa ofishin ƴan sanda da ke Eke.

Yayin da ya yi Allah-wadai da harin, kamfanin ya tabbatar wa da jama’a cewa yana aiki tare da hukumomin tsaro domin ganin an kuɓutar da fasinjojin da direban cikin koshin lafiya.

Ƴan sanda sun yi bayani

A halin da ake ciki kuma, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Sewuese Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Mai magana da yawun bakin rundunar ƴan sandan ta ce an tura jami’an tsaro na musamman, sojoji da ƴan sa-kai zuwa yankin.

"Sun yi sintiri a cikin daji kuma sun ceto wani da ake kira Paul Terna, wanda ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane."

- SP Sewuese Anene

'Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji
'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan sanda sun samu nasara kan ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga.

Jami'an tsaron sun yi raga-raga da ƴan bindigan bayan sun farmaki manoma a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Ƙatsina.

Ƴan sandan sun kuma samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin manoman da ƴan bindigan suka sace a harin da suka kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng