Ruwa Ya Yi Gyara: Shanun N100m Sun Mutu Sakamakon Tsawa da Walkiya
- An yi wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a jihar Ogun da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya
- Tsawa da walƙiyar da aka riƙa yi yayin ruwan saman sun yi sanadiyyar mutuwar shanun kuɗinsu sun kai N100m
- Ɗan uwan mai shanun ya miƙa ƙoƙon bararsa ga gwamnatin jihar kan ta tallafa musu su rage raɗaɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - An samu asarar shanun da kuɗaɗensu sun kai N100m sakamakon tsawa da walƙiya a jihar Ogun.
Tsawa da walƙiyar dai an yi su ne a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙaramar hukumar Odeda ta jihar Ogun.

Asali: UGC
Baale na Osara, Obantoko, dake Abeokuta, Cif Wasiu Afolabi, ya tabbatarwa jaridar The Punch cewa shanu 32 ne suka mutu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shanu sun mutu a jihar Ogun
Cif Afolabi ya ce la'akari da yadda lamarin ya faru, wasu bokaye masu bauta wa Sango za su zo a ranar Litinin, domin gudanar da wasu al’adu don sassauta bala’in kafin a binne gawarwakin shanun, wanda jami’an gwamnati daga jihar za su sa ido a kai.
Ya ƙara da cewa kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Daisi Elemide da shugaban ƙaramar hukumar Odeda, Dr. Afolashade Adeyemo, sun ziyarci yankin domin jajanta wa makiyayan da kuma duba halin da ake ciki da idonsu.
"Mun kammala taro da ƴan sanda kuma Fulani makiyaya suna wurin. Jami’an tsafta daga ƙaramar hukuma za su binne gawarwakin shanun a yau Litinin, bayan bokayen Sango sun kammala gudanar da al’adunsu. Al’ummar yankin za su ɗauki nauyin kuɗin wannan al’ada."
"Kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Daisi Elemide da Shugabar Ƙaramar Hukumar Odeda, Dr. Afolashade Adeyemo, sun zo domin duba abin da ya faru da kuma yi wa Fulanin jaje."
"Darajar kuɗin shanun da suka mutu ya kai kusan Naira miliyan 100. Wadannan shanu manya ne kwarai. Kuna iya ganin gaskiyar hakan a cikin faifen bidiyon da ke yawo. Babbar asara ce matuƙa."
- Cif Wasiu Afolabi
Rahotanni sun ce tsawa da walkiya ne suka kashe shanun da misalin ƙarfe 12:00 na rana a ranar Asabar, yayin wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
An nemi gwamnati ta kawo ɗauki
A ɗaya ɓangaren kuma, babban ɗan’uwan mai shanun, Hassan Momodu, ya roƙi gwamnatin jihar da ta tallafa wa ɗan’uwansa da ya yi asarar komai sakamakon wannan ibtila’in, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Momodu, wanda ya yabawa gwamnatin jihar da ‘yan sanda bisa matakan da suka ɗauka tun bayan afkuwar lamarin, ya bayyana cewa bala’in ya bar ɗan’uwansa ya koma babu komai a hannunsa.

Asali: UGC
Ya ce ɗan uwan na sa yanzu ba shi da abin ciyar da iyalansa da kuma wasu mutane sama da 20 da ke dogara da harkar kiwon shanun don samun na abinci.
"Mai shanun ƙanina ne. Shi ke riƙe da nauyin ƴan uwansa gaba ɗaya. Ban da iyalansa, akwai fiye da mutane 20 da ke samun abinci daga wannan sana’ar, amma yanzu ya rasa komai."
“Darajar kuɗin shanun tana dab da Naira miliyan 100. Don haka muna roƙon gwamnati da ta duba yiwuwar taimaka wa matashin nan ya farfaɗo da harkokinsa. Mun yarda cewa annoba ce daga Allah, amma tallafin gwamnati zai iya rage raɗaɗin."
- Hassan Momodu
Barayi sun sace ragon layya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ɓarayi sun tsallaka har cikin gida sun sace ragon layya a birnin Abuja.
Ɓarayin dai sun yi wannan aika-aikar ne lokacin da suka fahimci mai gidan ya fita waje a lokacin.
Masu halin ɓerar dai sun tsallaka cikin gidan ne da tsakar rana sannan suka yi awon gaba da ragon layyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng