Barau: Bayan Kwankwaso, An Bukaci Tinubu Ya Zabo Mataimaki daga Kano

Barau: Bayan Kwankwaso, An Bukaci Tinubu Ya Zabo Mataimaki daga Kano

  • Sunan Sanata Barau Jibrin ya fito a cikin jerin mutanen da ake shawartar mai girma Bola Tinubu ya zaɓa a matsayin abokan takararsa a 2027
  • Wata ƙungiya ta buƙaci shugaban ƙasan da ya ɗauki Sanata Barau a matsayin mataimakinsa a babban zaɓen 2027 da ake tunkara
  • Ta nuna cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan yana da ƙwarewar da ake buƙata don riƙe muƙamin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - An ba shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan mutumin da zai ɗauka a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2027.

An shawarci Tinubu da ya ɗauki mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a matsayin abokin takararsa na mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Ana son Barau ya zama mataimakin Tinubu a 2027
An shawarci Tinubu ya dauki Barau a matsayin abokin takara a 2027 Hoto: @barauijibrin, @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta rahoto cewa wannan kiran ya fito ne daga wata ƙungiya mai suna Northern Nigeria’s Progressive Youths Assembly (NNPYA).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta jita-jita da cece-kuce kan kujerar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki, sakamakon jita-jitar cewa ana iya maye gurbin Kashim Shettima, wanda ke riƙe da mukamin a yanzu.

An ba Bola Tinubu shawara daukar Barau

"Wannan shawara ba za ta kasance gurguwa ba, idan shugaban Najeriya Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi Sanata Barau Jibrin a matsayin abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027."
“Domin zaɓar mutum mai karɓuwa a siyasance a matsayin abokin takara, tabbas ɗaya ne daga cikin mafi kyawun dabarun siyasa da kowane ɗan takara zai iya amfani da shi."

- Ƙungiyar NNPYA

Ƙungiyar ta ce, sun daɗe suna da yakinin cewa Shugaba Tinubu, wanda ya shahara wajen ƙwarewa da wayewa a harkokin siyasa, ba zai yi wata-wata ba wajen yin lissafi daidai na zaɓar Sanata Barau Jibrin a matsayin abokin takararsa.

Sannan ƙungiyar ta kuma fayyace cewa, ko da yake Kano ita ce asalin jihar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, wato Rabi’u Musa Kwankwaso, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u har 517,341.

Ta ce hakan kusan ninki biyu ne na waɗanda aka kaɗawa jam'iyyar APC a jihar Borno inda Kashim Shettima ya fito.

An shawarci Tinubu ya zabi Barau a matsayin abokin takara
Ana son Tinubu ya dauki Sanata Barau a matsayin abokin takara Hoto: @barauijibrin
Asali: Facebook

An yaba ƙwazon Sanata Barau Jibrin a Kano

“Kar mu manta, sakamakon ƙwazon Sanata Barau ne jam’iyyar APC ta samu waɗancan ƙuri’un a kusan dukkan zaɓukan da aka gudanar."
"Domin a cikin dukkanin masu neman kujerun majalisar wakilai daga yankin Sanata Barau na Kano ta Arewa, mutum ɗaya ne kawai ya sha kaye a hannun jam’iyyar adawa.”
“A wannan lokaci mai matuƙar mahimmanci da siyasa ke cike da ruɗani, dole ne Shugaba Tinubu ya yi taka-tsantsan wajen zaɓar abokin takararsa domin kada ya zaɓi wanda ba zai dace da kujerar ba.”
"Sanata Barau Jibrin mutum ne da ya taso cikin kyakkyawar tarbiyya, bai taɓa zagi ko raina wani shugaba ba, na baya ko na yanzu, domin yana da ra’ayin cewa ba wanda ya kamata a raina shi ko a wulakanta shi, komai shekarunsa, jinsi ko matsayinsa a cikin al’umma."

- Ƙungiyar NNPYA

Kwankwaso na iya maye gurbin Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara hasashen cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iga ɗaukar Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.

Majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya maye gurbin Kashim Shettima.

Wata majiya ta nuna cewa batun Kwankwaso ya maye gurbin Shettima ya fara samun karɓuwa a wajen juha-jigan jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng