Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin kaca-kaca da ƴan ta'adda a jihar Sokoto. Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda masu yawa tare da ƙwato makamai.
Sojojin kungiyar Ansaru sun fara fitowa karara a gabashin Birnin gwari. ‘Yan ta’adda sun fara fitowa daga jeji, su na auren 'yan matan mutanen gari.
Jami'an tsaro a jihar Neja sun yi musayar wuta da wani ƙasurgumin ɗan ta'adda da ake zargin ɗan Boko Haram ne a birnin Minna, inda suka ƙwato makamao masu yawa.
Mu na da labari a Sokoto, Garba Moyi Isa ya hakura da kujerar da aka ba shi na shugaban kwamitin kafa jami’an tsaron sa kai, ya yi murabus a karshen makon nan.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin galaba akan ƴan ta'adda a sassan daban-daban na ƙasar nan. Sojojin sun kuma cafke masu taimakawa ƴan ta'addan.
Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya bukaci bai wa mutane damar siyan bindiga a kasuwa don kare kansu kamar yadda 'yan bindiga ke yi a kasuwanni.
Wata babbar kotu mai zamanta a ƙaramar hukumar Potiskum ta shirya sanya ranar da za ta yanke hukunci kan sojojin da suka halaka Sheikh Goni Aisami.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe miyagun ƴan ta'adda da suka addabi bayin Allah a jihar Kaduna. Sojojin sun kuma fatattakiɓda yawa daga cikinsu.
Wani 'dan majalisa ya kai kuka game da yadda ‘yan bindiga su ka addabe su, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta cece su daga hannun ‘yan bindiga da ke barna a Neja.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari