Hankalin Iyaye Ya Tashi Bayan Ganin Daliban da Aka Dauke Sun Rike AK47 a Bidiyo

Hankalin Iyaye Ya Tashi Bayan Ganin Daliban da Aka Dauke Sun Rike AK47 a Bidiyo

  • Kungiyar PTAN tayi magana bayan ganin daliban makarantar Gwamnatin Yauri rike da AK-47 a wani bidiyo
  • Shugaban kungiyar, Haruna Danjuma yace ya kamata gwamnati ta dage domin kubutar da wannan dalibai
  • ‘Yan bindiga su na yunkurin aurar da ‘Yan makarantar da su kayi garkuwa da su, ko su jefa su a aikin ta'adi

Kebbi - Shugaban kungiyar PTAN ta iyaye malamai a Najeriya, Haruna Danjuma ya nuna damuwarsa a kan ‘yan makarantan da ke hannun ‘yan ta’adda.

Vanguard ta kawo rahoto cewa Alhaji Haruna Danjuma ya damu ganin yadda wasu daliban makarantar Yauri a jihar Kebbi suke tsare tun a shekarar 2021.

A wani bidiyo da yake ta yawo a shafin sada zumunta, an ga wata dalibar makarantar dauke da bindigar AK-47 da casbin harsahi cikin gungun ‘yan bindiga.

Miyagun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da daliban suna barazanar amfani da ‘yan matan makarantar da suka yi garkuwa da su a matsayin sojojinsu.

An ji ‘yan bindigan suna cewa tun da iyayen yaran sun gagara yin hobbasa domin kubutar da su, za su shigar da su cikinsu da nufin su rika yin ta’adi.

Iyaye su tashi tsaye - PTAN

Ganin halin da ake ciki, shugaban PTAN ya nuna takaici da tashin hankalin da suka shiga, yana mai kira ga iyayen yaran su yi kokarin kai masu agaji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bagudu
Gwamnan jihar Kebbi Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto Haruna Danjuma yana cewa rayuwar ‘yan matan na cikin babban hadari idan irin wadannan miyagu za su rika ba su manyan makamai.

Kira na musamman ga gwamnatoci

Danjuma ya yabawa gwamnatin tarayya kan kokarin da tayi wajen ceto fasinjojin jirgin da aka dauke watanni shida da suka wuce a hanyar Kaduna-Abuja.

Ganin wadannan mutane sun dawo gida a yanzu, Danjuma ya roki gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta ta dawo da hankalinta kan daliban.

Kungiyar ta PTAN tayi kira ga gwamnatin jihar Kebbi da tayi bakin kokarin ta ita ma wajen ganin wadannan kananan yara da ke karatu sun dawo gidajensu.

“Mu a matsayinmu na PTAN, mun nuna rashin jin dadinmu kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, na yaranmu da bindigogi suna neman taimako.
Muna kira gwamnatin tarayyar Najeriya, tayi amfani da hikima da dabara da salon da tayi amfani da su wajen ceto fasinjoji, domin kubutar da ‘daliban Yauri.”

An yi shahada a Zamfara

An ji wani mugun labari cewa 'Yan kananan yara da mata sun hallaka yayin tserewa ‘yan bindiga a wani kauyen Zamfara a tsakiyar makon da ya gabata.

Mutanen Birnin Waje a garin Bukkuyum sun tashi da harbe-harben bindigogi, don haka wasunsu suka shiga ruwa domin su bar kauyen, sai suka nutse.

Asali: Legit.ng

Online view pixel