Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP

Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP

  • Rundunar jami’an tsaro ta hadin guiwa na MNJTF sun bayyana damke mutum 40 dake samarwa ‘yan ta’addan ISWAP abinci mai yawan gaske
  • A jimilla, dakarun sun kama buhu 364 na wake, buhu 102 na masara, buhu 12 na kifi, jakuna 9 da sauran nau’ikan kayan abinci da aka nufi tafkin Chadi dasu
  • An gano cewa ‘yan ta’addan na karfafa guiwar mazauna yankin su yi noma inda suke karbar N30,000 na haraji tare da buhunan kayan abinci na zakkah

Borno - Dakarun MNJTF sun ce sun kama mutum 40 dake samarwa ‘yan ta’addan ISWAP kayan aiki a yankin tafkin Chadi.

ISWAP Suppliers
Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP. Hoto daga @zagazolamakama
Asali: Twitter

Aikin sirrin da dakarun sashi na uku na Monguno suka yi a ranar 11 ga watan Oktoban 2022 yasa an kama wadanda ake zargin kuma an samo buhu 64 na wake, buhu biyu na masara da sauran kayan abinci masu tarin yawa, Zagazola Makama ya rahoto.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

Za a mika kayan abincin ne zuwa yankin Tumbu dake tafkin Chadi inda maboyar ‘yan ta’addan take.

Bayan wani samamen da dakarun suka kai, an sake kama wasu buhu 300 na wake da buhu 100 na masara wanda a take dakarun suka lalata su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, dakarun bataliya ta 68 dake sintirin hadin guiwa wuraren yankunan Malam Fatori, Badamari, Bari, Korarawan duk samu nasarar kwace buhu 12 na kifi da jakuna 9 wadanda ake zargin ana amfani dasu ne wurin kai wa ‘yan ta’addan abinci.

‘Yan ta’addan suna assasawa mazauna yankunan yin noma domin su samu abincin da zasu cigaba da ci suna ta’addanci.

Mazauna yankin dake kamun kifi ana kallafa musu N30,000 na haraji kuma ‘yan ta’addan na karbar wasu a matsayin zakkah.

Idan za a tuna, Zagazola Makama ya rahoto yadda mazauna yankunan suka kafa kungiyoyin hadin kai kuma suka kafa sansanoni a wuraren Zannarida Hausari, Kutukungulla, Sigir, Kusuma, Bangur da Kirta duk a karamar hukumar Marte.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Wadanda suka fito daga Monguno kuma suka ratsa ta Bulwa Bakindam, Namaro, Gratai, Garin Karfe duk suna sansani a Tumbun Dila, Daban Gajere, Kwatan da Daban Masara.

Za a iya samunsu a wuraren Dawashi, Alisharafti Garin Malam Ya’u, Shaibori, Tumbun Yashi, Daban Shata, Kwatan Mali, Shuwarin, Daban Wanzam da Tumbun Rago.

Akwai masunta dake zuwa daga Sokoto, Kebbi, Kano da Zamfara ta Hadejia, Jigawa, Nguru, Gaidam zuwa Gigeme a jamhuriyar Nijar.

Jama’ar Kamaru suna shigowa ta Bulgaram, Cikka, Guma, Maltam yayin da ‘yan Najeriya ke hadewa dasu ta Kogi daga Yola.

Da yawan farar hula na shigowa daga Madagali ko Michika a jihar Adamawa zuwa Mokolo zuwa Bulangowa Waza da Doron Liman.

ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoninsu a Yankunan Zamfara, Gwamnatin Jiha ta Koka

A wani labari na daban, mambobin kungiyar ISWAP an gano suna kafa sansanoni a wuraren kauyen Mutu dake yankin Mada ta karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Daily Trust ta rahoto cewa, kwamitin gurfanarwa na laifukan da suka hada da ‘yan bindiga da mambobin kwamitin tsaro da sirri, Dr Sani Shinkafi ya bayyana hakan a wani taro a Gusau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel