‘Yan Ta’addan ISWAP sun Kai Harin Tsakar Dare Kan Sojoji, Sun Sha Luguden Wuta

‘Yan Ta’addan ISWAP sun Kai Harin Tsakar Dare Kan Sojoji, Sun Sha Luguden Wuta

  • Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun fatattaki ‘yan ta’addan ISWAP da suka kai musu farmakin cikin dare a jihar Borno
  • An gano cewa ‘yan ta’addan sun tsinkayi garin Mafa dake arewa maso gabashin Borno a motocin yaki da babura
  • Majiyar tsaro ta sanar da yadda sojojin suka budewa ‘yan ta’addan wuta wanda hakan yasa dole suka arce tare da barin mugun nufinsu

Borno - Dakarun sojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar dakile harin da aka kai musu a daren Litinin a karamar hukumar Mafa dake arewa maso gabashon jihar Borno, Zagazola suka gano.

Sojojin Najeriya
Dakarun OPHK sun Kai Harin Tsakar Dare Kan Sojoji, Sun Sha Luguden Wuta. Hoto daga BBC.Com
Asali: Getty Images

An tattaro cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargin mambobin ISWAP ne sun tsinkayi garin Borno a motocin yaki da babura inda suka fara kai harin da ruwan wuta a kan dakarun.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata Majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama, kwararre a ganni kiyasi da yaki da ta’addanci a tafkin Chadi, cewa dakarun sun bankado harin da ‘yan ta’addan suka kai musu.

Majiyar tace:

“Sun yi yunkurin kai farmaki ta Charly Papa 1 amma an bankado mugun nufinsu. Tuni aka lallasa ‘yan ta’addan.
“Dole tasa suka ja da baya tare da tserewa tare da barin mummunan nufinsu. Babu wanda aka raunata a bangaren dakarun.”

- Majiyar tace.

Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga

A wani labari na daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama mota dankare da kayan abinci da za a kaiwa ‘yan bindigan dake da maboya a Dangulbi a karamar hukumar Maru ta jihar, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Bindige Mutum 1, Wasu 18 Sun Jigata a Arangamar ‘Yan Daban PDP da APC a Zamfara

A wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu yasa hannu a ranar Laraba, ‘yan sandan sun damke mutum takwas dake kai wa ‘yan bindiga bayanai, harsasai carbi 250 na AK47 da shanun sata 47.

An kama direban babbar motar yayin da yake kana hanyar kai wa ‘yan bindiga abinci a Maru, Anka da Gusau dake yankin dajin Dangulbi da Magami.

“Miyagun kwayoyin sun hada da allurar Penta, kwayoyin tramadol, allurorin chloroquine, kwayoyin exzol da kwalayen giya. An samu turamen atamfofi biyu duk a motar.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel