An Kashe Sojan Dake Shiga Tsakani Don Sulhunta Rikicin Manoma da Makiyaya a Jigawa

An Kashe Sojan Dake Shiga Tsakani Don Sulhunta Rikicin Manoma da Makiyaya a Jigawa

  • Wasu da ba'a sani ba sun kashe ɗaya daga cikin sojojin da suka je raba faɗan manoma da makiyaya a yankin Guri, jihar Jigawa
  • Ana zargin wasu baƙin makiyaya da kashe sojan, tuni hukumomi suka duƙufa don gano waɗanda suka aikata ɗanyen aikin
  • Shugaban ƙaramar hukumar Guri, Musa Muhammad, yace hukumomi da dama sun yi Allah wadai da kisan sojan

Jigawa - Wani Soja dake kokarin sasanta rikicin Manoma da Makiyaya a ƙaramar hukumar Guri ta jihar Jigawa ya rasa rayuwarsa ranar Laraba.

Mazauna yankin sun bayyana cewa makiyaya ne suka kashe sojan, waɗanda basu ga maciji da manoman yankin.

Sai dai jaridar Premium Times tace har yanzu bata tantance sahihancin wannan ikirarin ba amma makasan sojan sun yi awon gaba da Bindigarsa.

Sojojin Najeriya a bakin aiki.
An Kashe Sojan Dake Shiga Tsakani Don Sulhunta Rikicin Manoma da Makiyaya a Jigawa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Mazauna yankin sun ce sojan mai suna, Danlami Ɗanjuma, na cikin tawagar Sojojin da suka kai ɗauki bayan kiran gaggawa daga ƙauyen Gagiya lokacin da makiyaya suka kutsa gonakin mutane.

Kara karanta wannan

Wani Ibtila'i Ya Yi Ajalin Mutum 30 da Suka Gudo Wa Harin Ta'addancin Yan Bindiga a Zamfara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ƙaramar hukumar Guri, Musa Muhammad, yace hukumomi ciki harda al'ummar Fulani sun yi Allah wadai da kisan sojan kuma sun baza komar kame makasan da nemo bindigar.

Shugaban yace:

"Ya rasu a bakin aiki, sun je yankin ne da nufin daƙile faɗan da ka iya aukuwa tsakanin makiyaya da manoma amma bisa rashin sa'a wasu suka kashe shi."
"Makiyaya sun matsa kaimi wajen kiyo biyo bayan Ibtila'in ambaliyar ruwa da ake fama da ita wanda ya shafi wuraren kiyo da gonaki."
"Sojoji sun yi saurin zuwa wurin ne domin kwantar da hankula bayan Makiyaya sun fasa gonakin mutane."

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Muhammad ya ƙara da cewa mutanen da ake zargi da aikata wannan ɗanyen aiki , "Baƙin makiyaya ne," waɗanda suka saba zuwa shekara-shekara suna neman wurin kiyo.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Jagoran Al'umma a Jihar Arewa

Shugaban ƙaramar hukumar yace a halin yanzu hukumar soji da sauran hukumomin tsaro sun duƙufa bincike kan lamarin.

Legit.ng Hausa ta gano cewa Guri da maƙociyarta ƙaramar hukumar Kirikasamma a Jigawa, Allah ya albarkace su da ƙasar noma mai kyau da kuma kiyo.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Shugaban Al'umma a Jihar Filato

Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Sanannen jagoran al'umma, Gashon Leks, a yankin ƙaramar hukumar Mangu, jihar Filato.

Mazauna ƙauyen Daika, inda lamarin ya faru sun nuna damuwarsu saboda mutumin yana fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel