Sabuwar Kotun Soji Za Ta Yanke Wa Wasu Sojoji 68 Shari'a A Sokoto

Sabuwar Kotun Soji Za Ta Yanke Wa Wasu Sojoji 68 Shari'a A Sokoto

  • Rundunar sojin Najeriya ta sanar da shirin hukunta dakarun ta 68 saboda samun su da aikata laifuk daban daban
  • Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Uwem Bassey da ke kuma jagorancin Rundunar ’Hadarin Daji’ ya bayyana haka lokacin da yake kaddamar da kotun
  • Janar Bassey ya bukaci alkalan da za suyi shari’ar da su tabbatar da adalci da bin doka kan zargin da ake yi wa sojojin kasancewarsu wadanda suka hidimtawa kasarsu

Jihar Sokoto - Za a gurfanar da dakaru da sojojin Najeriya sittin da takwas a kotun sojoji kan zarginsu da aikata laifuka daban-daban, Daily Trust ta rahoto.

Dakarun sojoji
Sabuwar Kotun Soji Za Ta Yanke Wa Wasu Sojoji 68 Shari'a A Sokoto. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Facebook

Da ya ke kaddamar kwamitin na mambobi 12 a ranar Laraba, Babban kwamandan Runduna ta 8, Sokoto, Manjo Janar Uwem Bassey, ya ce ana zargin sojojin sun aikata laifukan ne yayin atisayen "Hadarin Daji" da ake yi don fatattakan yan bindiga a jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi da Katsina.

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma, ya ce yana kira ga mambobin kotun su darraja tsarin yi wa kowa adalci.

Kalamansa:

"Dole kotun ta tabbatar cewa gaskiya ta fito ta hanyar nazarin dukkan hujojin da aka gabatar.
"Domin dole a yi wa dukkan wadanda suka so yi wa kasarsu hidima adalci."

Ya bada tabbacin cewa kotun ta sojojin za ta yi aiki ne da tsarin adalci kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulki ta shekarar 1999.

Manjo Janar Bassey ya kara da cewa kotun ba za ta yarda da wani katsalandan ba.

Ya bukaci mambobin kotun su tabbatar ba a bata lokaci ba yayin shari'ar.

A bangare guda, lauyan wanda aka yi kara, Barrista Uwadiae, ya bayyana cewa yana fatan kotun za ta yi adalci.

Hotunan Yadda Sojoji Suka Kama Wasu Mata da Ke Jigilar Kaya Ga Boko Haram

Kara karanta wannan

Ummita: Kotu ta Dage Sauraron Shari'ar 'Dan Chana da Ya Halaka Budurwarsa Saboda Rashin Tafinta

A wani rahoton, Dakarun Bataliya ta 195 na Operation Hadin Kai, sun cafke wasu mutum 7 da ke jiglar kaya ga 'yan ta'addan Boko Haram a wajen Maidugiri, babban birnin jihar Borno.

Wadanda aka kama sun hada da; Hadiza Ali, Kelo Abba, Mariam Aji, Kamsilum Ali, Ngubdo Modu da Abiso Lawan, da dai sauransu, Leadership ta ruwaito.

A cewar wani rahoton sirri da Zagazola Makama ya samu daga manyan majiyoyin soja, an gano wadanda ake zargin dauke da tarin kaya da aka tanada domin kai wa ‘yan ta’addar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel