Dakarun Sojin Najeriya Sun Dira Maboyar ‘Yan Bindiga Sun Halaka Masu Yawa a Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya Sun Dira Maboyar ‘Yan Bindiga Sun Halaka Masu Yawa a Kaduna

  • Jajirtattun dakarun sojin Najeriya karkashin rundunat Operation Whirl Punch sun kai samame maboyar ‘yan bindiga dake titin Kaduna zuwa Abuja
  • Kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana, dakarun sun ragargaji miyagun kuma yanzu haka duba dajika ake yi
  • An yi kira ga al’ummomin al’ummomin yankunan Abasiya zuwa Amale dake Kachia da su guji taimakon wadanda suka gani da raunikan bindiga don wasu sun tsere

Kaduna - A kokarin da dakarun soji suke yi na zuwa har maboyar ‘yan bindiga, sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Whirl Punch sun halaka ‘yan bindiga a wurare daban-daban a wuraren titin Kaduna zuwa Abuja.

Sojojin Najeriya
Dakarun Sojin Najeriya Sun Dira Maboyar ‘Yan Bindiga Sun Halaka Masu Yawa a Kaduna. Hoto daga punchng.com
Asali: Twitter

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, dakarun sun yi aiki kan bayanan sirri inda suka fita sintiri zuwa yankin Abasiya zuwa Amale dake gabashin Polewire a karamar hukumar Kachia inda suka yi wa ‘yan bindigan ruwan wuta.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ruwan wutan, dakarun sun rinjayi ‘yan bindigan kuma daga bisani sun tarwatsa maboyarsu.

Har a halin yanzu dakarun suna kakkabe dukkan yankin yayin da suka samu gawawwakin ‘yan bindiga biyu da suka halaka.

An samo kayayyakin da suka hada da bindiga kirar AK47 daya, harsasai da wayar salula daya.

Kamar yadda takardar da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana, alamu na nuna cewa wasu ‘yan bindigan sun tsere da miyagun raunika kuma ta yuwu su nemi taimakon masana kiwon lafiya a yankin.

“A saboda haka muke kira ga mazauna yankin da su kiyayi taimakon duk wani da suka gani abun zargi, a maimakon hakan sun kai rahoto zuwa lambobi kamar haka: 09034000060, 08170189999.
“Za a sanar da jama’a kan duk wani cigaba dangane da hakan.”

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi

- Yace.

A wani cigaba da galaba da aka samu a kan ‘yan bindigan, Aruwan yace dakarun Operation Forest Sanity sun yi martani kan harin da aka kai wuraren Dende- Buruku a karamar hukuar Chikun.

Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP

A wani labari na daban, Dakarun MNJTF sun ce sun kama mutum 40 dake samarwa ‘yan ta’addan ISWAP kayan aiki a yankin tafkin Chadi.

Aikin sirrin da dakarun sashi na uku na Monguno suka yi a ranar 11 ga watan Oktoban 2022 yasa an kama wadanda ake zargin kuma an samo buhu 64 na wake, buhu biyu na masara da sauran kayan abinci masu tarin yawa, Zagazola Makama ya rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel