'Ba Ma'aikata Aka Zane Ba': Umahi Ya Magantu Kan Bidiyon Da Ya Bazu Inda Sojoji Ke Wa Wasu Bulala A Gabansa

'Ba Ma'aikata Aka Zane Ba': Umahi Ya Magantu Kan Bidiyon Da Ya Bazu Inda Sojoji Ke Wa Wasu Bulala A Gabansa

  • Injiniya Dave Umahi, gwamnan jihar Ebonyi ya ce bidiyon da ake yadawa da cewa ya sa an zane ma'aikatan gwamnati ba gaskiya bane
  • Kwamishinan labarai na Ebonyi, Orji, ya ce wadanda aka zane bata gari ne da ke son hana yan kwangila aiki da sunan dokar zama-a-gida
  • Ya kuma ce lamarin ya faru ne a kofar shiga filin tashi da saukan jiragen sama da ake aiki ba a gidan gwamnati ba kamar yadda bidiyon da aka yada ke cewa

Jihar Ebonyi - Gwamnatin Jihar Ebonyi ta ce bidiyon da aka yada da cewa gwamnan Jihar David Umahi, ya saka a zane wasu mazauna jihar ba haka lamarin ya ke ba, The Cable ta rahoto.

A ranar Talata, bidiyon ya bazu a dandalin sada zumunta da ke nuna gwamnan yana kallo a yayin da jami'an tsaro ke zane mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi karin haske kan bidiyonsa da aka gani yana umartar sojoji su zane ma'aikata a jiharsa

Dave Umahi
'Ba Ma'aikata Aka Zane Ba': Umahi Ya Magantu Kan Bidiyon Da Ya Bazu Inda Sojoji Ke Wa Wasu Bulala A Gabansa. Hoto: @TheCableNg.
Asali: Twitter

Bata gari ne masu son aiwatar da dokar zama-a-gida, ba ma'aikatan gwamnati ba - Orji

Da ya ke martani kan lamarin, Uchenna Orji, kwamishinan labarai na Ebonyi, ya ce mutanen da ke bidiyon ba ma'aikatan gwamnati bane amma 'bata-gari" da suka yi yunkurin tabbatar da dokar 'zama-a-gida a hanyar shiga filin tashin jiragen sama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce akasin abin da rahotannin da suka bazu ke cewa, lamarin ya faru ne yayin da gwamnan ya tafi duba ayyukan da aka yi a filin jiragen sama amma ba gidan gwamnati bane.

Orji ya ce ba a dauki ma'aikatan gwamnati su rika aiki a filin jiragen saman ba.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Muna son sanar da al'umma cewa bidiyon da ake yadawa wasu bata gari ne da suka yi yunkurin rufe kofar shiga filin jirgin sama don firgita wadanda ke aiki a wurin da kuma yunkurin kunyata gwamnan wanda ya tafi ziyarar duba aiki, da sunan aiwatar da dokar zama-a-gida a filin jirgin saman a ranar Talata 4 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

"Idan za a iya tunawa a baya bata garin sun yi yunkurin kai wa wadanda ke aiki a filin jirgin hari amma aka dakile su."

Sanarwar ta Orji ta bukaci al'umma su yi watsi da bidiyon da aka sauya abin da ya faru ake yadawa da nufin bata wa gwamnan suna, yana mai cewa aikin makiya ne.

Gwamna Umahi Na APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Bola Tinubu Yana Motsa Jiki

A wani rahoton, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce ɗan takarar shugaban kasa ƙarƙashin APC na nan a raye kuma ba ya bukatar gamsar da mutane cewa yana raye.

Gwamna Umahi ya yi wannan furucin ne yayin hira a shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin din Channels tv ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel