Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa

Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Babban Lambar Yabo Na Kasa

  • An fitar da cikakken jerin sunayen wadanda za a bawa lambar yabo na kasa a Najeriya inda suka dara 400
  • Tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin T.Y Buratai na cikin wadanda za a karrama
  • Za a karrama Buratai da lambar yabo na Commander of the Order of the Federal Republic (CFR)

FCT, Abuja - Tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya kuma jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, T.Y. Buratai ya shiga jerin wadanda za su samu lambar yabo ta kasa na 'Commander of the Order of the Federal Republic', (CFR).

Tsohon shugaban sojojin da wasu fitattun yan Najeriya guda 436 ne za a karrama da lambar yabon a wannan shekarar.

Buratai
Shugaba Buhari Ya Karrama Buratai Da Lambar Yabo Na Kasa Ta CFR. Hoto: Yusuf Tukur Buratai.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Buhari Zai Karrama Sarkin Kano, Sarkin Zazzau Da Wasu Sarakuna 18 Da Lambar Girma Ta Kasa

Kamar yadda Legit.ng ta gano, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata 11 ga watan Oktoba zai gabatar da lambar yabon da wadanda aka zaba a gidan gwamnati, Abuja.

"Buratai ya cancani lambar yabon" - Dr Abubakar

Da ya ke martani kan batun, na hannun damar jakadan, Dr Mohammed Abubakar ya ce Buratai ya cancanci karramawar.

Ya ce tsohon shugaban sojojin ya taka muhimmin rawa wurin kawo zaman lafiya a kasa duk da kallubalen da aka fuskanta a baya.

Dr Abubakar ya ce:

"Bari in fayyace maka gaskiya ina murna da wannan lambar yabon da Shugaba Muhammadu Buhari zai bawa wasu yan Najeriya.
"Ina cikin wadanda suke fatan ganin Shugaban Kasa ya karrama Janar Buratai da lambar yabo na kasa. Saboda na san sadaukarwar da ya yi, an nada shi shugaban sojoji don kare iyakokin kasar mu da tsaron cikin gida.
"Ta yi wu bai warware dukkan matsaloli da kallubale ba na sojojin amma ya inganta shi fiye da yadda ya tarar da shi. Don haka, ina son in ce ya cancanci wannan lambar yabo na kasa ta CFR."

Kara karanta wannan

UNICAL: Jerin manyan farfesoshi 5 da suka mutu a ci gaba da yajin aikin ASUU

Buhari zai karrama Abba Kyari, Tunde, Okonjo-Iweala da Wasu 437 da Lambar Girma

A bangare guda, wani rahoto da Premium Times ta fitar a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba 2022, ya nuna Ngozi Okonjo-Iweala tana cikin wadanda za a karrama.

Za a ba shugabar kungiyar WTO da sauran wadanda aka zaba wannan lambar yabo ne a ranar 11 ga watan Oktoba. Za ayi bikin a fadar shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel