Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin Kwantan Bauna da Boko Haram Suka kai Musu, Sun yi Musu Lugude

Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin Kwantan Bauna da Boko Haram Suka kai Musu, Sun yi Musu Lugude

  • Mayakan ta’addancin Boko Haram sun dasawa sojojin dake wucewa bam duk a cikin harin kwantan bauna a Borno
  • Sai dai reshe ya juye da mujiya yayin da sojojin suka dakile harin tare da far wa ‘yan ta’addan inda suka budewa ‘yan ta’addan wuta
  • A take suka halaka da yawa daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu sojoji suka jigata sannan motarsu kirar Hilux ta lalace

Dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai a Borno, jaridar TheCable ta rahoto.

Harin kwantan baunan da ‘yan ta’addan suka kai an bankado shi yayin da dakarun suka budewa ‘yan ta’addan wuta tsakanin Kumshe da Bama.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin Kwantan Bauna da Boko Haram Suka kai Musu, Sun yi Musu Lugude. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, an kashe da yawa cikin ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun Kama Wiwi ta N4m wacce Za a Kai wa ‘Yan Ta’adda a Yobe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addan sun dasa bam wanda suka biye shi da harbin bindiga.

“‘Yan ta’addan sun dasa abu mai fashewa kuma suka biye shi da harbe-harben bindiga wanda a take zakakuran sojojin suka dakile shi.”

- Wata majiya tace.

“Rundunar ta musamman ta dakile farmakin inda ta halaka ‘yan ta’addan masu tarin yawa amma babu wanda aka rasa a bangaren sojojin.
“Mota kirar Hilux ta sojojin ce aka lalata yayin da wasu sojoji suka samu miyagun raunika yayin arangamar amma yanzu haka ana basu taimako a hedkwatar birged dake Bama.”

Wannan cigaban na zuwa ne bayan makonni da rundunar Operation Hadin Kai suka halaka ‘yan Boko Haram shida a Borno yayin wani harin kwantan bauna da suka kai kauyen Kayamla kusa da birnin Maiduguri.

Hakazalika, a ranar 11 ga watan Satumba, dakarun sun halaka ‘yan Boko Haram masu tarin yawa a wani samame da suka kai kasuwar Daula dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Hankalin Iyaye Ya Tashi Bayan Ganin Daliban da Aka Dauke Sun Rike AK47 a Bidiyo

Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo

A wani labari na daban, dubun Shugaba kuma gagararren ‘dan ta’addan jihar Kaduna, Ali Dogo, ta cika inda sojoji suka aika shi lahira tare da wasu mayakansa sakamakon luguden wuta ta jiragen yaki da aka yi musu a karamar hukumar Giwa ta jihar.

An gano cewa dakarun rundunar Operation WHIRL Punch ne suka a kwanakin karshen mako da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel