Borno: Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda 31, Sun Damke 70 a Borno

Borno: Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda 31, Sun Damke 70 a Borno

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa sojoji sun halaka ‘yan ta’adda 31 tare da cafke wasu 70 a arewa maso gabashin jihar Borno
  • Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana cewa daga cikin 70 da suka shiga hannu, 60 suna samarwa ‘yan ta’addan kayan bukata ne
  • A wani cigaba na daban, dakarun sun ragargaza ‘yan ta’addan a Gargash da Ngauri dake Bama inda suka yi musu ruwan wuta har maboyarsu

Hedkwatar tsaro ta kasa a ranar Alhamis, tace dakarun Operation Hadin Kai sun halaka kusan mayakan Boko Haram da na ta’addancin ISWAP 31 tare da kama wasu 70.

Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, daraktan fannin yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ya sanar da hakan a Abuja yayin jawabi kan nasarorin da dakarun suka samu a makonni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji Sun Ragargaza Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Zamfara, Chire

Ya kara da cewa daga cikin 70 din da aka kama a yankin arewa maso gabas, 60 daga cikinsu duk ‘yan ta’adda suka samarwa kayan abinci, makamai da man fetur da sauransu.

Sai dai rundunar sojin bata yi magana kan Gargash da Ngauri ba dake karamar hukumar Bama inda sojojin sama suka halaka wasu ‘yan ta’addan a maboyarsu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP

A wani labari na daban, Dakarun MNJTF sun ce sun kama mutum 40 dake samarwa ‘yan ta’addan ISWAP kayan aiki a yankin tafkin Chadi.

Aikin sirrin da dakarun sashi na uku na Monguno suka yi a ranar 11 ga watan Oktoban 2022 yasa an kama wadanda ake zargin kuma an samo buhu 64 na wake, buhu biyu na masara da sauran kayan abinci masu tarin yawa, Zagazola Makama ya rahoto.

Kara karanta wannan

Dakarun MNJTF Sun Kama Mutum 40 da Buhu 364 na Wake, 102 na Masara Zasu Kai wa ‘Yan ISWAP

Za a mika kayan abincin ne zuwa yankin Tumbu dake tafkin Chadi inda maboyar ‘yan ta’addan take.

Bayan wani samamen da dakarun suka kai, an sake kama wasu buhu 300 na wake da buhu 100 na masara wanda a take dakarun suka lalata su.

Hakazalika, dakarun bataliya ta 68 dake sintirin hadin guiwa wuraren yankunan Malam Fatori, Badamari, Bari, Korarawan duk samu nasarar kwace buhu 12 na kifi da jakuna 9 wadanda ake zargin ana amfani dasu ne wurin kai wa ‘yan ta’addan abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel