Kwankwasiyya
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kudin jarrabawar dalibai 55,000 don rubuta jarrabawar Hukumar NECO a jihar don inganta ilimi.
Gwamnatin Kano ta soma rushe gine-ginen da ke filin Kwalejin Fasaha ta Kano a Salanta. Hakan ya jawo rigima ta Barke tsakanin Masu Rusau da Masu Gidaje a jiya.
Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin a fara shirin tura yaran Kano zuwa jami’o’in kasashen Duniya. Gwamnatin Kano ta dawo da tsarin Kwankwasiyya da aka saba da shi
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi nadin mukamai. Abba Gida Gida ya ba Salisu Yahaya Hotoro, Salisu Muhammad Kosawa mukaman SA.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce har yanzu bai yanke shawarar sauya sabbin masarautun da tsohon gwamna Ganduje ya yi ba, inda ya ce duk jita-jita ce.
Majalisar dokokin jihar Kano, a zamanta na ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, ta sahale wa gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin hadiman da zasu tama shi aiki 20.
Gwamnan Kano ya bada umarni rugurguza shatale-talen gaban gidan Gwamnati. Sannan an cigaba da rushe gine-ginen shagunan da ke filin Masallacin Idi na Ƙofar Mata
Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Osun, ta yi martani mai zafi akan Abdullahi Umar Ganduje bayan ya yi barazanar marin jagoranta, Kwankwaso.
An gayyaci Rabiu Kwankwaso zuwa Aso Villa a kan rushe-rushen da ake yi, Kwankwaso ya fadawa Bola Tinubu Abdullahi Ganduje ya rika kwashe filayen talakawan Kano
Kwankwasiyya
Samu kari