An Gina Kwankwasiyya Ne Kan Bautarwa Da Bauta, In Ji Jigon APC A Kano

An Gina Kwankwasiyya Ne Kan Bautarwa Da Bauta, In Ji Jigon APC A Kano

  • Ciyaman din Kano Municipal, Faizu Alfindiki, ya ce ya fita daga tafiyar Kwankwasiyya ne don an gina ta kan 'bautarwa da bauta'
  • Jigon na jam'iyyar APC mai mulki a Kano ya ce wannan tsarin ya sabawa tsarin cigaban demokradiyya
  • Ya yi wannan jawabin ne yayin tarbar wasu yan jam'iyyar NNPP ta suka sauya sheka zuwa APC a jihar Kano, wadanda suka ce salon jagorancinsa ya sa suka shigo jam'iyyar

Jihar Kano - Shugaban tafiyar Gawuna/Garo 2023 a Kano Central, Faizu Alfindiki, ya ce ya fita daga tafiyar Kwankwasiyya ne saboda an gina ta kan 'bautarwa da bauta' ne.

Alfindiki ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata a lokacin da wasu matasa daga gundumar Zaitawa suka fita daga NNPP suka dawo APC mai mulki a jihar, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Kwankwaso
Kwankwasiyya Ya Ginu Akan Bautarwa Da Bauta, In Ji Jigon APC Na Kano. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Akidar Kwankwasiyya ta sabawa cigaban demokradiyya - Alfindiki

Ya bayyana cewa akidar tafiyar ta sabawa dorewa da ci gaban dimokuradiyya a kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban tafiyar na Kano Central, wanda shine ciyaman na Kano Municipal ya ce:

"Munyi shekaru tare da Kwankwasiyya, mun yi hidima, a kowanne yanayi amma babu wani sakayya da muka samu saboda sadaukarwar mu."

A cewarsa, jam'iyyar APC karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje a shekara 7 da suka gabata ta bullo da sabuwar hanya na sakawa Kano da mutanen garin.

Ciyaman din na Kano Municipal ya ce:

"Hujja ta farko na ayyukan Dr Ganduje ana iya gani a titunan mu da gidajenmu duba da yawan mutane da aka karfafawa gwiwa."

Ya yaba wa wadanda suka sauya shekan

Ya kuma jinjinawa wadanda suka dawo jam'iyyar saboda hangen nesa, yana mai cewa da alamu tawagar Gawuna/Garo 2023 suna kan hanyar yin nasara.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Gwamna Ya Bukaci Jam'iyyar PDP Ta Kori Gwamna Mai Ci Ƙan Wasu Dalilai

Tunda farko, a jawabinsa, Muniru Yakasai, wanda ya jagoranci wadanda suka sauya shekar ya ce salon tafiya tare da kowa da Alfindiki ke yi a Kano Municipal yasa suka shigo jam'iyyar.

Ya ce:

"A halin yanzu, Gawuna shine wanda ya fi cancanta ya jagoranci jihar Kano saboda zai dora kan nasarorin da Ganduje ya samu na habbaka jihar."

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.

Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164