Zaben 2023: Kwankwaso Ya Bayyana Ranar Da Zai Gabatar Da Manufofinsa Ga Yan Najeriya

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Bayyana Ranar Da Zai Gabatar Da Manufofinsa Ga Yan Najeriya

  • Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce zai fitar da manufofinsa ga yan Najeriya a ranar 1 ga watan Nuwamban 2022
  • Mr Ladi Johnson, mai magana da yawun kwamitin kamfen din shugaban kasa na NNPP ya bayyana hakan
  • Johnson ya ce Kwankwaso, a ranar 31 ga watan Oktoba zai fara tattauna manufofin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar kafin kaddamarwa a ranar 1 ga watan Nuwamba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya zabi ranar 1 ga watan Nuwamban 2022, a matsayin ranar bayyana manufofinsa na shugabancin kasa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ta yi martani kan gargadin tsaro da Amurka da Birtaniya suka yi tana mai cewa kwamitin na da kwamitin tsaro wacce za ta tabbatar da lafiyar magoya bayanta yayin tattaki.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ta karewa Atiku, gwamnan Arewa na PDP da dattawan jiharsa sun ce ba sa yinsa

Kwankwaso
Zaben 2023: Kwankwaso Ya Bayyana Ranar Da Zai Gabatar Da Manufofinsa Ga Yan Najeriya. Hoto: @NigerianTribune.
Asali: UGC

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP, Ladi Johnson ne ya bayyana cikin wata sanarwa mai lakabin 'Dage kaddamar da manufofin dan takarar shugaban kasa da taron zagayowar ranar haihuwar RMK karo na 3', za a yi ne ranar 1 ga watan Nuwamban 2022.

A cewarsa, taron zagayowar ranar haihuwar RMK karo na 3 a ranar 31 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa dagewar ya zama dole ne don jam'iyyar ta tuntubi masu ruwa da tsaki da mambobinta a fadin kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Taron zagayowar ranar haihuwar na RMK karo na 3, wanda ke cikin abubuwan da aka shirya don cikar mai girma Dr Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 66, yanzu za a yi ne a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba 31, 2022, misalin karfe 10 na safe a cibiyar taro na A-Class Park and Events Centre, Wuse II Abuja."

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi

Kakakin jam'iyyar na NNPP ta cigaba da cewa:

"A ranar kuma, mai girma zai gana da ciyamomin jihohi na jam'iyyya, yan takarar gwamna da sanatoci da sauran masu ruwa da tsaki don su duba manufofinsa ga Najeriya da Yan Najeriya, yayin da za a gabatar da manufofin a ranar Talata 1 ga watan Nuwamban 2022."

Sai dai, Mr Johnson ya ce kwamitin za ta iya tunkarar duk wani kalubalen tsaro yayin kamfen din ta.

Ya kara da cewa NNPP ta san da batun gargadin tsaron kuma za ta rika la'akari da lamarin tsaron yayin kamfen dinta.

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

A wani rahoton, mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Asali: Legit.ng

Online view pixel