Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna zai maida hankali a kan harkar ilmi idan ya karbi mulkin Najeriya
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na Jam’iyyar NNPP ya kaddamar da manufofinsa ga al’umma a Abuja
  • Kwankwaso zai tsawaita wa’adin jarrabawar JAMB kuma ya magance rashin zuwa makaranta

Abuja - A ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba 2022, Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da manufofin da ya yi tanadi idan ya karbi shugabancin Najeriya.

Rabiu Musa Kwankwaso mai takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya nuna gwamnatinsa za ta bada muhimmanci ga ilmi, Punch ta fitar da rahoton nan.

‘Dan takaran yace zai tabbata daliban Najeriya sun samu damar shiga makarantu gaba da sakandaren kasar nan kyauta, ba tare da sun biya sisin kobo ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Abin da Buhari Ya Fada Mani Yayin da Na Nemi Ya Zakulo Mani Mataimakina

Kwankwaso yace idan ya yi nasara a 2023, gwamnatinsa za ta cire kudin da ake biya wajen zana jarrabawowi irinsu WAEC, NECO, NBAIS, da kuma NABTEB.

Sakamakon JAMB zai yi shekaru hudu

Baya ga cire kudin jarrabawa da za ayi, ‘dan siyasar ya sha alwashin tsawaita wa’adin JAMB ta yadda za a iya shafe shekara hudu ana amfani da jarrabawar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto ‘Dan takaran yana cewa an kafa wadannan hukumomi ne domin taimakawa harkar ilmi, don haka babu dalilin a maida su na tatso kudi.

Rabiu Kwankwaso
Bikin kaddamar da manufofin Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Ilmin zamani zai samu gata

Tsohon gwamnan na Kano yace muddin mulkin Najeriya ya dawo hannunsa, zai kawo karshen yara miliyan 20 da ba su zuwa makarantar boko a kasar nan.

Legit.ng Hausa ta saurari jawabin Sanata Kwankwaso mai neman zama shugaban kasa a 2023, inda ta ji ya yi alkawarin gina dakunan karatu 500, 000 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jigon Siyasa Ya Hango Faɗuwar Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Zai Gaji Buhari a 2023

"A gwamnatinmu, babu yaron da za a hana damar rubuta jarrabawar WAEC, NECO, JAMB da sauransu, saboda tsadar kudin rajista da yin jarrabawa.
Wadannan jarrabawa za su kasance kyauta, haka zalika fam din shiga makarantun gaba da sakandare. Gwamnatinmu za ta dauki nauyin hukumomin.
Batun cewa jarrabawa ta tashi aiki bayan shekara daya zai zo karshe.
A gwamnatin Kwankwaso, JAMB za tayi shekaru hudu ana amfani da ita, za a bukaci TEI su karbi sakamakonta. - Rabiu Musa Kwankwaso

Tinubu da halaccin Arewa

A lokacin da Bola Tinubu ya rude game da zaben fitar da gwani, an rahoto 'dan siyasar yace Gwamnonin APC na Arewa suka goyi bayan a ba shi tuta.

‘Dan takaran shugaban kasar ya bayyana yadda suka yi da shugaban kasa da kuma abin da ya sa ya dauko Sanata Kashim Shettima domin suyi takara tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel