Zaben 2023: Jerin Jihohin Da Kwankwaso Da Obi Basu Da Rundunar Yakin Neman Zabe

Zaben 2023: Jerin Jihohin Da Kwankwaso Da Obi Basu Da Rundunar Yakin Neman Zabe

  • Duk da shaharar Peter Obi na jam'iyyar LP da Kwankwaso na NNPP, sai sun yi da gaske a zaben 2023
  • Kwankwaso da Peter Obi basu da yan takara a wasu jihohi biyar da mazabun Sanata kimanin 20
  • Hakan ya sa basu da rundunar yakin neman zabe a lunguna da sakon wadannan jihohi

Yan Najeriya musamman matasa na yunkurin tunkude jam'iyyun All Progressives Congress APC da People's Democratic Party PDP a zabukan da zasu gudana a 2023.

Cikin kankanin lokaci, dan takaran jam'iyyar Labour Party LP, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), sun samu karbuwa wajen yan Najeriya.

Amma a yanzu da zabe ya kusanto, wadannan yan takaran biyu basu da yan takaran gwamna a wasu jihohi.

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023

Yayinda LP ba tada dan takaran gwamna a jiha 1, NNPP ba tada dan takaran gwamna a jihohi 4.

Jam'iyyar Labour Party dan takara a jihar Ogun, yayinda NNPP ba tada dan takara a Borno, Cross River, Kebbi da Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obi Kwankwaso
Zaben 2023: Jerin Jihohin Da Kwankwaso Da Obi Basu Da Rundunar Yakin Neman Zabe Hoto; Obi/Kwankwaso
Asali: Facebook

Basu da yan takaran Sanata sama da 20

Wadannan jam'iyyu biyu basu da sojojin yakin neman zabe a wadannan mazabu saboda rashin isassun mambobi.

A zaben majalisar dattijai, Labour Party ba tada yan takara a mazabu 28 cikin 109.

A majalisar wakilai kuwa, NNPP ba tada yan takara biyu cikin 360 yayinda LP na tada yan takara a mazabu 128.

Ga jerin mazabun da basu da yan takara:

Bauchi Ta Arewa;

Bayelsa Ta Gabas

Bayelsa Ta Yamma

Mazabun Borno 3

Delta ta Arewa

Delta ta tsakiya;

Mazabun Ekiti 3;

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi dalilan da suka sa Kwankwaso ya ki martaba gayyatar dattawan Arewa

Jigawa South West

Jigawa North West;

Mazabun Katsina 3,

Mazabun Kebbi 3;

Kogi West;

Mazabun Lagos 3;

Niger North;

Ondo Central

Ondo South;

Sokoto North,

Yobe North

Yobe East.

Asali: Legit.ng

Online view pixel