Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

A makon nan ‘dan takaran 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso zai yi bikin cika shekara 66 da haihuwa a Duniya

Sanata Rabi'u Kwankwaso tsohon Gwamna ne wanda yake neman shugabancin Najeriya a zaben 2023

A wannan rahoto, mun kawo maku bayanai a game da rayuwa da gwagwarmayar siyasar Rabiu Kwankwaso

1. Mukamai a siyasa

Kusan a tarihin siyasar Najeriya, babu wanda ya rike manyan mukamai irin Rabi'u Musa Kwankwaso. ‘Dan takaran ya taba zama Gwamna na shekara takwas.

Baya ga haka ya rike kujerar Ministan tarayya, sannan ya je majalisar dattawa a 2015. Tun a shekarar 1992 kuwa ya zama na biyu a zauren ‘dan majalisar wakilai.

2. Tashi a gidan sarauta

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ko da ya zama babban ‘dan siyasa, Rabiu Kwankwaso ya tashi ne a gidan sarauta. Mahaifinsa Marigayi Musa Saleh ya dade yana Hakimci a garin Madobi a Kano.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe

Tsohon Gwamnan shi ne babban ‘dan Majidadin Kano (daga baya ya zama na kasar Karaye).

3. Siyasa tun yana makaranta

Tun yana yaro a makarantun Gwarzo da Wudil, ‘dan takaran ya fara nuna alamun shugabanci. Zuwa lokacin da yake Difloma, ya shiga cikin shugabannin dalibai.

Yayin da Kwankwaso ya je jami’ar fasaha ta Loughborough a Ingila, sai da ya jagoranci dalibai, kujerar da babu wani ‘dan kasar waje da ya taba rikewa a lokacin.

4. Sha’awar ilmin zamani

Kwankwaso ya yi fice a wajen ganin matasa sun samu ilmin zamani. Gwamnatinsa ta tura yara 2500 karatu a jami’o’i, ko bayan ya bar mulki ya cigaba da yin hakan.

Shi kan shi ya koma makaranta inda ya samu shaidar Digirin PhD a jami’ar Sharda da ke Indiya.

Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

5. Ajiye aikin Gwamnati

A shekarar 1975 Injiniya Rabiu Kwankwaso ya fara aiki da hukumar ruwa ta WRECA a Kano, amma ya yi caca, ya ajiye aikin na sa a 1991, ya fada harkar siyasa.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP ya Raba Kayan Tallafin Ga Wadanda Masifa ta Auka Masu

6. Zuwa majalisa

Rabiu Musa ya shiga siyasa kuma ya yi nasarar zama ‘dan majalisar wakilan tarayya a 1992 a jam’iyyar SDP, har ya yi nasarar zama mataimakin shugaban majalisa.

7. Zama Gwamna da rasa zabe

A Mayun 1999 aka rantsar da Rabiu Kwankwaso a matsayin Gwamna bayan ya lashe tikitin PDP. ‘Dan shekara 43 a lokacin, ya ba manyan ‘yan siyasar Kano mamaki.

Wani abin mamaki shi ne PDP ta rasa zaben gwamnan Kano a 2003. Kwankwaso bai kalubalanci nasarar Ibrahim Shekarau a kotu ba, a karshe aka nada shi Minista.

8. Dawo-dawo

Har ila yau, Injiniya Kwankwaso ya sake zama Gwamna a Kano bayan zaben 2011. Mutane suna cewa a lokacin da ya yi mulki na biyu, jihar ta ga cigaba na bada misali.

A karshen wa’adin Gwamna ya bar PDP, ya nemi takarar kujerar shugaban kasa a APC. Daga baya ‘dan siyasar ya zama Sanatan Kano ta tsakiya da kuri’a mai yawa.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

9. Alakarsa da Abdullahi Ganduje

Abokan hamayyarsa a lokacin da ya fara takara sun hada da Abdullahi Ganduje, haka aka yi a zaben 2007. Kwankwaso ya rika aiki da Ganduje a siyasance.

A sanadiyyar Kwankwaso ne Ganduje ya rike kujerar tarayya. Bayan ya mika masa mulki a 2015, sai sabani ya shiga tsakaninsu har Kwanwaso ya bar APC.

10. Takaran 2019 da 2023

A Yulin 2018 Sanata Kwankwaso ya koma PDP, bayan nan ya shiga neman takarar shugaban kasa, amma Atiku Abubakar ya samu gagarumar nasara a kan su.

Daga baya tsohon Ministan ya sake ficewa daga PDP, ya dauko jam’iyyar NNPP. Yanzu shi ne ‘dan takaran shugaban kasa a jam’iyya mai alamar kayan dadi a 2023.

Aminu Dabo yana nan a APC

Kun samu labari cewa jigon APC, Aminu Dabo ya nesanta kan shi da takarar Peter Obi, yace an sa sunansa a kwamitin kamfeb LP ba tare da an tuntube shi ba.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

Arch. Aminu Dabo ya fadawa Peter Obi cewa kyau ya hakura da neman kujerar shugabancin Najeriya a 2023, ya marawa Bola Tinubu baya a APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel