Rikici Ya Yi Tsami, Alhassan Doguwa ya Fasa-bakin Kakakin APC a Gaban Jama'a

Rikici Ya Yi Tsami, Alhassan Doguwa ya Fasa-bakin Kakakin APC a Gaban Jama'a

Bayan abin da ya faru tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo, an sake yin wata arangama

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya naushi Ahmad Aruwa a lokacin da ya zo gidansa yayin da ake yin taro

Kakakin na APC ya je gidan tsohon Mai gidansa ne domin yah ana shi barin APC, a karshe bai ji da dadi ba

Kano - Jim kadan da rigima tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo, sai aka ji ‘dan majalisar ya aukawa wani ‘dan jam’iyyarsa ta APC.

Daily Nigerian ta samu labari cewa Honarabul Alhassan Ado Doguwa ya aukawa Sakataren yada labarai na APC na reshen jihar Kano, Ahmad Aruwa.

An yi taro a gidan Alhassan Doguwa domin karrama mahaifiyarsa wanda ta zama fitila a rayuwarsa, a nan ne babban ‘dan siyasar ya ci karo da Aruwa.

Kara karanta wannan

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

Shugabannin jam’iyyar APC a Kano sun samu labarin karya cewa Doguwa yana shirin sauya-sheka biyo bayan abin da ya faru da shi da Hon. Garo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Aruwa ya yi karambani?

A dalilin haka aka nemi Abdullahi Abbas a matsayinsa na shugaban APC na reshen jihar, ya je gidan Doguwa domin ya hana shi barin jam’iyya mai mulki.

Da Abbas ya ki yarda ya lallashi ‘dan majalisar wakilan tarayyar, sai Ahmad Aruwa ya kama hanya ya je, a matsayinsa na tsohon hadimansa jigon na APC.

Alhassan Ado Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta ci karo da bidiyon yadda abin ya faru, wani 'dan jarida daga Kano, Malam Ameenu Kutama ya wallafa faifen a Twitter a safiyar Laraba.

Wata majiya da ta san halin da ake ciki, ta shaidawa jaridar Hon. Doguwa yana yin ido hudu da Aruwa a taron, sai ya hankada shi, ya kuma nushe shi.

Kara karanta wannan

Abin da ya Haddasa Fadanmu da Murtala Garo a gidan Gawuna - Alhassan Doguwa

A dalilin nushin da ‘dan majalisar na Tudun-Wada/Doguwa ya kai wa kakakin jam’iyyar ta APC, ya yi masa rauni jini ya rika tsiyaya daga bakinsa.

“Ya bayyana Aruwa a matsayin ma-ci amana, ya kuma bukaci ya bar masa gida. Aruwa ya bar gidan yana kuka, bakinsa yana jini.

- Majiya

Doguwa v Rabiu Suleiman-Bichi

An kuma rahoto cewa kafin nan, Doguwa ya kira Rabiu Suleiman-Bichi da wani babba a APC ta salula, yana yi masu kashedin cewa zai yi maganinsu.

Ana tunanin ‘dan siyasar ya fusata da tsohon sakataren gwamnatin na Kano ne saboda ya bada shawarar a fadawa Mai girma Gwamna ya hukunta shi.

Fadan Doguwa da Garo

A wani rahoto da muka fitar, an ji Alhassan Ado Doguwa ya yi bayanin yadda rigima ta kaure tsakaninsa da Murtala Sule Garo a gidan 'dan takarar gwamna.

‘Dan majalisar yace Murtala Garo ne ya fara zagin shi, ya nemi ya yi fada da shi daga zuwa inda su ke zama, tsohon kwamishinan ya kayata wannan zargi.

Kara karanta wannan

Rai Bakin Duniya: Kasa da Awa 24 da Daura Aurensa, Ango Yace ga Garinku

Asali: Legit.ng

Online view pixel