Gwamna Buni Ya Faɗi Bashin da Tinubu Ke Bin Ƴan Arewa game da Zaɓen 2027

Gwamna Buni Ya Faɗi Bashin da Tinubu Ke Bin Ƴan Arewa game da Zaɓen 2027

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi magana kan sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a Arewacin Najeriya a 2027
  • Buni ya ce Bola Tinubu na bin yan Arewa bashin goyon bayan wa’adi na biyu saboda irin taimakon da ya taba bayarwa a baya
  • Gwamnan ya bayyana haka a Kaduna yayin kaddamar da rabon tallafin kudi na naira biliyan 1.2 da manyan motocin shinkafa 100

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana damar da Bola Tinubu ke da shi a zaben 2027.

Mai Mala Buni, ya bukaci Arewa ta marawa Bola Ahmed Tinubu baya domin samun wa’adi na biyu a shekarar.

Buni ya bukaci Arewa ta sake ba Tinubu dama a 2027
Bola Tinubu da Gwamna Mai Mala Buni da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Mai Mala Buni.
Source: Facebook

Wannan na cikin wata sanarwa da Hadiminsa, Mamman Mohammed ya wallafa a shafin Facebook wanda wakilin Legit Hausa ya leko.

Kara karanta wannan

Yunwa a Arewa: Tinubu ya ware tireloli 100 na abinci, makudan kudi ga jihohi 19

Tallafin da Bola Tinubu ya ware ga Arewa

Buni ya bayyana haka ne a Kaduna yayin kaddamar da rabon tallafin Naira biliyan 1.2 da manyan motocin shinkafa 100 ga mabukata a jihohin Arewa 19 kafin bikin sallah.

An shirya tallafin ne ta hannun ofishin Oluremi Tinubu tare da hadin gwiwar Ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Kabiru Masari.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokawa kan ci gaba da shan wahala da yan kasar ke ciki tun bayan hawan Tinubu.

Gwamna Buni ya roki yan Arewa kan Tinubu

Gwamna Buni ya ce shugaban kasa Tinubu ya dade yana marawa ‘yan takarar shugaban kasa daga Arewa baya a lokuta daban-daban saboda hadin kai da kishin kasa.

Gwamnan ya tuna yadda Tinubu ya goyi bayan marigayi Shehu Yar’Adua, Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari a zabukan baya, yana cewa yanzu Arewa ta rama masa.

Ya ce a shekarar 1992, Tinubu ya goyi bayan marigayi Shehu Yar'Adua maimakon dan uwansa Bayarabe, Olu Falae, duk da kasancewarsu daga Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada sabon Ministan lantarki bayan Adelabu ya yi murabus

Gwamna ya fadi alherin Tinubu ga Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya a birnin Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Kokarin da Tinubu ya yi ga Arewa

Buni ya kara da cewa Tinubu ya marawa Atiku Abubakar baya a zabe, sannan ya goyi bayan marigayi Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2015.

Sanarwar ta ce:

“A shekarar 2007, Shugaba Tinubu ya kuma marawa Atiku Abubakar baya a burinsa na zama shugaban ƙasa.
“Haka kuma ya goyi bayan marigayi Muhammadu Buhari a shekarar 2015, saboda haka ya cancanci samun goyon bayan Arewa domin wa’adi na biyu a mulki.”

Sanarwar ta ce Gwamna Buni ya bayyana cewa Arewa ya kamata ta nuna godiya ga Tinubu ta hanyar mara masa baya a 2027.

Ya bayyana abubuwan da Tinubu ya kawo na ci gaba a Arewacin Najeriya inda ya ce hakan yana bukatara saka masa da alheri.

Gwamna Buni ya nuna wanda zai gaje shi

A wani labarin, mun ba ku labarin cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Yobe sun bayyana wanda suke so ya tsaya masu takarar gwamna a zaben 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Abba ya kinkimo aiki, za a kashe sama da N21bn don jiƙa Kanawa da ruwan sha

Rahotanni sun nuna cewa sun bayyana matsayarsu ne yayin wani zama da suka yi a birnin tarayya Abuja tare da gwamna Mai Mala Buni.

Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana dalilan zaben Baba Malam Wali a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar APC takara a zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.